Tsohon Shugaban APC Ya Hango Faduwar Tinubu, Ya Fadi Wadanda Za Su Iya Lashe Zaben 2027
- Cif John Odigie-Oyegun ya bayyana cewa alamu sun nuna Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai samu damar tazarce ba a zaben 2027
- Tsohon shugaban APC ya nuna kwarin gwiwar cewa ADC za ta karbe mulkin Najeriya domin ceto kasar daga halin da ta shiga
- Dattijon 'dan siyasar ya kuma bayyana cewa idan ADC ta kafa gwamnati, za ta tabbatar da rikon amana da adalci da kowane 'dan kasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, John Odigie-Oyegun, ya bayyana cewa hadakar ADC na shirin karbe mulki daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Cif John Oyegun ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga wakilai a babban taron ADC na kasa da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan
Jigon ADC ya 'gano' halin da APC ke ciki, ya fadi hadin da zai kai Tinubu ƙasa a 2027

Source: Facebook
John Oyegun ya hango faduwar Bola Tinubu
A rahoton da Daily Trust ta tattaro, tsohon shugaban na APC ya ce alamu sun nuna Tinubu ba zai kai labari ba, inda ya nuna kwarin gwiwa cewa ADC ta gama shirin karbe mulki.
“Mun shirya karbe Aso Rock, kuma ba za a ci gaba da tafiya yadda aka saba ba,” in ji shi.
Mista Oyegun ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a kawo sauyi a shugabancin kasa domin ceto Najeriya daga halin da ta shiga.
Ya kuma yi martani ga masu sukarsa cewa ya taba kasancewa a cikin tsarin da APC take tafiya a yanzu, inda ya ce hakan ba zai hana shi neman gyara ba.
Oyegun ya nuna damuwa kan halin da ake ciki
Tsohon gwamnan Jihar Edo ya nuna damuwa kan yadda Najeriya ke da yalwar albarkatun kasa amma al’umma na ci gaba da fuskantar wahala, yana mai cewa hakan na nuni da gazawar shugabanci.
“Kasarmu ce mafi girma daga nahiyar bakar fata a duniya, Allah ya halicce mu da manufa, amma duba abin da muka yi da kasar,” in ji shi.
Oyegun ya kara da cewa shugabannin ADC sun kawo sabon fata ga ‘yan Najeriya, yana mai cewa jam’iyyar na shirin fara abin da ya kira aikin ceton kasa, cewar The Cable.

Source: Twitter
Wane shiri ADC ke yi na ceto Najeriya?
Ya jaddada cewa idan ADC ta karbi mulki, za ta mayar da hankali wajen tabbatar da rikon amana da kuma hukunta duk wanda ya yi kuskure a gwamnati
“Duk wanda ya yi aiki mai kyau za a yaba masa, wanda kuma ya yi ba daidai ba, duniya za ta san abin da ya aikata,” in ji shi
A karshe, Oyegun ya nuna kwarin gwiwa cewa jam’iyyar ADC na kan hanyar karbe mulki a matakin tarayya, yana addu’ar Allah ya ba su karfin gwiwar aiwatar da abin da ya dace domin ceto kasar.
Momodu ya nemi hada tikitin Atiku-Obi
A wani rahoton, kun ji cewa jigo a jam'iyyar hamayya ta ADC, Dele Momodu ya bayyana cewa APC mai mulki na cikin rudani gabanin babban zaben 2027.
Momodu, ya bayyana goyon bayansa ga yiwuwar haɗa tikitin shugaban ƙasa tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi a karkashin inuwar jam'iyyar ADC.
Ya bayyana yakinin cewa hada wadannan mutane biyu a tikitin takarar shugaban kasa da mataimakinsa zai taimaka wajen kayar da APC a cikin sauki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

