"Tsuntsu Mai Sauya Sheka": Ganduje Ya Ce Siyasar Kwankwaso Ta Zo Ƙarshe

"Tsuntsu Mai Sauya Sheka": Ganduje Ya Ce Siyasar Kwankwaso Ta Zo Ƙarshe

  • Tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce sauya shekar Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa ADC na sabon abu ba ne
  • Ganduje, wanda tsohon makusancin Kwankwaso ne ya bayyana tsohon ubangidansa a matsayin tsuntsu mai yawan sauya sheka
  • Ya ce ba su kallon hadakar ADC a matsayin abin tashin hankali, musamman saboda akwai abin da zai wargaza su nan gaba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ADC ba za ta iya kawo wani gagarumin sauyi a siyasar Najeriya ba.

Ganduje ya ce sauya shekar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa ADC ba wata barazana ba ce ga APC ko kuma siyasar jihar Kano, yana mai cewa tsohon gwamnan ya saba sauya jam’iyya a tsawon rayuwarsa ta siyasa.

Kara karanta wannan

"Abba ne jagora a Kano": Ganduje ya yi magana kan naɗa Garo mataimakin gwamna

Ganduje ya ce siyasar Kwankwaso ta zo karshe
Tsofaffin gwamnonin Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Dr. Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso/Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Twitter

A wata hira da BBC, Ganduje ya bayyana Kwankwaso a matsayin mutum mai yawan sauya sheka, yana kwatanta shi da tsuntsu mai sauka a wurare daban-daban.

Martanin Ganduje kan sauya shekar Kwankwaso

A yayin zantawar, Ganduje ya jaddada cewa babu wata barazana ko tasiri da sauya shekar Rabi'u Musa Kwankwaso za ta yi wa APC ko siyasar Kano gaba ɗaya.

Ya kara da cewa a ganinsa, alamu na nuna cewa siyasar Kwankwaso na dab da zuwa ƙarshe, lamarin da ya sa ya koma ADC, jam’iyyar da ya ce tana fama da rikice-rikice na cikin gida.

A kalamansa:

"Ba wata barazana, shi ba tsuntsu ne ba? Ya sauka nan, ya sauka can, ya sauka nan?"
"Ba wata barazana, ƙarshen siyasa ne ya zo, saboda haka ya tafi wata jam’iyya wacce haɗaka ce."
"Kuma wannan haɗakar, kowa burinsa ya tsaya takarar shugaban ƙasa, kuma wannan shi ne zai wargaza jam’iyyar."

Kara karanta wannan

Ganduje ya faɗi abin da ya kori Gawuna daga APC, ya taɓo batun butulci a siyasar Kano

Ganduje: "Gwamnoni na tururuwar shiga APC"

Ganduje ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da samun yawaitar gwamnonin jihohi da ke komawa jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan na nuna ƙarfin jam’iyyar a halin yanzu.

Ganduje ya ce gwamnoni na shiga APC bisa ra'ayin kansu
Tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Facebook

Ya ce ba a taɓa samun irin wannan yanayi ba a tarihin Najeriya, inda jam’iyya mai mulki ke da goyon bayan gwamnonin jihohi sama da 30 a lokaci guda.

Tsohon shugaban na APC ya musanta zargin cewa ana tilasta wa gwamnoni sauya sheka zuwa jam’iyyar domin kauce wa matsin lamba ko barazana.

A cewarsa, dukkanin gwamnonin da ke sauya sheka suna yin hakan ne bisa ra’ayinsu da kuma abin da suke gani na ci gaba a gwamnatin APC.

Ya kara da cewa gwamnonin suna jin daɗin yadda ake tafiyar da mulki a ƙarƙashin APC, wanda hakan ke kara jawo su shiga jam’iyyar ba tare da wata tsoro ko matsin lamba ba.

Ganduje ya magantu kan Gawuna

A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilin da ya sa aka gan shi da shugaban ƙasa a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi karatun ta natsu, ya gano dalilin da ya sa ake yawan samun mabarata a Arewa

Ganduje ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya kira shi domin tattauna rikicin siyasar Kano da ta dauki zafi musamman batun Nasiru Yusuf Gawuna.

Ya bayyana cewa sauya sheka da Harsuna ya yi zuwa ADC ra'ayinsa ne, babu wanda ya yi masa laifi kuma ba a samu sabani da shi a jam'iyya mai mulki ta APC ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng