Yadda 'Yan Bindiga Suka Je har Gida Suka Sace Babban Alkali a Arewacin Najeriya

Yadda 'Yan Bindiga Suka Je har Gida Suka Sace Babban Alkali a Arewacin Najeriya

  • Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da alkalin babbar kotun Kebbi, Mai shari'a Faruku Hassan Bunza, a gidansa da ke karamar hukumar Bunza
  • Iyalansa sun ce maharan sun bi shi tun daga Sokoto, sannan suka harbe-harbe kafin su tafi da shi kan babura
  • Lamarin ya kara tayar da hankali kan matsalar tsaro a Kebbi, duk da cewa Bunza ba ta cikin wuraren da hare-haren 'yan bindiga suka fi kamari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Wasu 'yan bindiga sun sace alkalin babbar kotun jihar Kebbi, Mai shari'a Faruku Hassan Bunza, a gidansa da ke kan titin Zogirma a karamar hukumar Bunza.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, jim kadan bayan alkalin ya dawo daga wata tafiya zuwa jihar Sokoto.

An ji yadda aka sace babban alkali a Arewacin Najeriya
Taswirar jihar Kebbi, inda aka sace wani babban alkali, Mai Shari'a Bunza. Hoto: UGC
Source: UGC

An yi garkuwa da babban alkali

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa maharan sun kutsa cikin gidansa bayan dawowarsa, inda suka yi ta harbe-harbe domin tsoratar da mazauna yankin kafin su yi awon gaba da shi.

Kara karanta wannan

Ba adalci: Kanawa sun yi martani da Gwamna ya raba filaye, N100m ga yan dangwale

Wata majiya ta ce babu wani daga cikin iyalansa da ya samu rauni, amma an sanar da jami'an tsaro da shugabannin babbar kotun jihar nan take bayan faruwar lamarin.

Yadda aka sace Mai shari'a Bunza

Dan'uwan alkalin, Malam Shehu Yusuf Bunza, ya bayyana cewa daya daga cikin 'ya'yan Mai shari'a, Abdullahi, ne ya kira shi ya sanar da abin da ya faru.

A cewarsa, kusan mutum bakwai dauke da makamai ne suka bi Mai shari'ar tun daga Sokoto har zuwa gidansa.

Shehu ya ce da isarsu gidan, maharan sun tambaye shi ko shi ne Mai shari'a Faruku Hassan Bunza. Ko da ya yi kokarin musanta hakan, suka yanke hukuncin cewa sun san shi ne mutumin da suke nema.

Bayan ya ci gaba da magana da su cikin Hausa, sai suka fara harbe-harbe tare da umartar shi ya kai su cikin dakunansa, amma ya ki saboda akwai matan aure a ciki.

Ya kara da cewa maharan sun kuma nemi ganin dansa Abdullahi, amma aka shaida musu cewa ba ya gida. Daga nan ne suka tilasta wa alkalin hawa babur suka tafi da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: An yanke wa mutum 3 hukuncin daurin rai da rai kan sace daliban Oyo

Iyalan sun tabbatar da cewa sun kai rahoton lamarin ga DPO na ofishin 'yan sanda da ke Bunza domin fara bincike da kokarin ceto shi.

Ana fuskantar kalubalen tsaro a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, inda aka sace wani babban alkali, Mai Shari'a Bunza. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kalubalen tsaro a Kebbi

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sace Mai shari'a Bunza ya zo ne bayan makamancin haka ya faru da Mai shari'a Ebiyerin Umokoro na babbar kotun jihar Bayelsa, wanda aka yi garkuwa da shi a watan Yunin 2025 kafin daga bisani a kubutar da shi bayan kwanaki 12.

Duk da cewa Kebbi ta sha fama da hare-haren 'yan bindiga, galibinsu sun fi shafar yankunan kudu da gabashin jihar da ke makwabtaka da dazukan Zamfara, Neja da Sokoto.

Sai dai wannan sabon lamari ya nuna yadda matsalar tsaro ke kara fadada zuwa sabbin yankuna da ba a saba samun irin wadannan hare-hare ba.

Martanin 'yan sanda kan sace alkali

Tun da fari, mun ruwaito cewa, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da sace Mai shari'a Faruku Hassan Bunza.

SP Bashir ya ce bayan samun rahoton sace shi, kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Umar Muhammad Hadejia, ya tura jami’an musamman da na leƙen asiri domin tabbatar da an ceto shi cikin koshin lafiya.

Wani babban jami’i a Babbar Kotun Jihar Kebbi, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin babban abin takaici ga bangaren shari’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com