Tsadar Man Jirgin Sama na Barazana ga Zuwa Hajjin 2026 a Najeriya

Tsadar Man Jirgin Sama na Barazana ga Zuwa Hajjin 2026 a Najeriya

  • An fara korafi game da yadda farashin man jirgin sama ya yi mummunan tashi a Najeriya da fargabar lamarin ya shafi aikin Hajjin bana
  • Wata kungiya mai alaka da hada-hadar jiragen sama ta ce matukar gwamnati ba ta shiga lamarin ba kudin aikin Hajji zai tashi sosai a kasar nan
  • Masu jiragen sama sun yi barazanar fara yajin aiki a Najeriya, inda suka ce wasu kamfanoni sun fara daina aiki saboda matsalar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Masu ruwa da tsaki a fannin zirga-zirgar jiragen sama sun yi kira ga gwamnati ta shiga tsakani kan tsadar man jirgin sama da ke kara tashi sama babu kakkautawa.

Kiran da kungiyar Concerned Aviation Stakeholders ta yi na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar kalubale mai girma wajen shirya aikin Hajjin 2026, musamman ta fuskar sufuri da kudi, sakamakon tsadar man jiragen sama.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya yi gargadi kan neman hana kamfen a jihohin Arewa 8

Yadda ake tafiya aikin Hajji daga Najeriy zuwa Makkah
Mahajjatan Kaduna na shirin shiga jirgi zuwa Saudiyya. Hoto: NAHCON
Source: Facebook

Batun tsadar man jirgin sama

The Nation ta wallafa cewa shugaban kungiyar, Alhaji Bukalti Usman Gamawa, ya bayyana cewa hauhawar farashin mai na ci gaba da zama barazana ga jigilar dubban alhazan Najeriya zuwa kasar Saudiyya.

Ya kara da cewa yawancin kamfanonin jiragen sama da aka dauka domin aikin Hajjin 2026 za su bukaci hayar karin jirage domin iya dauke mutane gaba daya.

Sai dai Gamawa ya ce da wannan tsadar man da ake fama da ita a yanzu, ribar da suke sa ran samu ta kusan gushewa gaba daya.

A cewarsa, akwai yiwuwar wasu kamfanonin su rika aiki ba tare da samun riba ba ko ma su yi asara, wato su yi zirga-zirga kamar kyauta bayan sun biya kudin haya da sauran kudin gudanarwa.

Punch ta wallafa cewa ya yi gargadi da cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba, wasu kamfanonin ba za su iya fara aiki daga Najeriya ko ci gaba da dawowa daga Saudiyya ba.

Kara karanta wannan

Kasar da ake ba 'yan mata da samari tallafi domin samun damar fara soyayya

Fargabar da ake yi kan Hajjin bana

Gamawa ya bayyana cewa duk da cewa Gwamnatin tarayya da na jihohi sun daina bada tallafin kai tsaye ga aikin Hajji, masu ruwa da tsaki na ganin dole ne a dauki matakin gaggawa kamar tsara farashi.

Shugaban kungiyarya bayyana cewa akwai bukatar tallafawa wajen samun kudin waje, ko samar da man fetur ta hanyoyi na musamman domin kauce wa rushewar shirin.

Mahajjata na aikin Hajji a Saudiyya
Masu aikin Hajji na dawafi a dakin Ka'aba. Hoto: Inside the Haramain
Source: Facebook

Ya jaddada cewa idan ba a samu hadin kai da daukar mataki cikin gaggawa daga gwamnati, hukumomi, kamfanonin jirage da ‘yan kasuwa ba, akwai yiwuwar kudin kujera zuwa Hajji ya tashi fiye da kima ko gaza aikin gaba daya.

Rahotanni sun nuna cewa a lokacin da aka kulla yarjejeniyoyin Hajji, farashin litar man jirgin sama a Najeriya yana kusan N1,000.

A yanzu kuma, a irin Abuja, Kano, Legas, Maiduguri, Yola, Sokoto da Birnin Kebbi, farashin man ya kai har N3,000, wanda ke nuni da karin sama da kashi 200.

Kara karanta wannan

Amurka ta koma tekun Asiya, ta kwace manyan jiragen ruwan Iran makare da mai

Amurka ta yi gargadi game da batun Hajji

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Amurka ta yi gargadi kan aikin Hajjin bana saboda barazanar tsaro da ake fama da ita a Gabas ta Tsakiya.

Yakin da aka yi tsakanin Iran Amurka da Isra'ila na tsawon kwana 40 ya haifar da matsalolin tsaro da suka shafi kasashen duniya.

Amurka ta gargadi 'yan kasarta game da halin da yankin ke ciki, tare da kira ga 'yan kasarta su sake nazari game da zuwa Hajjin bana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng