2023: Pat Utomi yayi magana game da rade-radin sabuwar jam'iyyar siyasa a ranar 1 ga watan Oktoba

2023: Pat Utomi yayi magana game da rade-radin sabuwar jam'iyyar siyasa a ranar 1 ga watan Oktoba

  • Farfesa Pat Utomi, ya yi watsi da rade-radin cewa shi da wasu manyan ‘yan Najeriya suna shirin sanar da sabuwar jam’iyyar siyasa a ranar 1 ga watan Oktoba
  • Utomi ya bayyana kungiyar ta Rescue Nigeria Project (RNP) a matsayin mai ra'ayin samar da kwararrun shugabanni a mulki, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba
  • Ya kuma bayyana kudirinsu na son ganin kasar ta inganta

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Farfesa Pat Utomi, ya yi watsi da rade-radin cewa shi da wasu manyan ‘yan Najeriya suna shirin sanar da sabuwar jam’iyyar siyasa a ranar 1 ga watan Oktoba.

An alakanta Utomi a kafafen yada labarai da “runduna ta uku,” da ake kira Rescue Nigeria Project (RNP) domin baiwa 'yan Najeriya madadin jam'iyyar APC mai mulki, da babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta sake dage babban taron jam'iyya na jihohi zuwa wani lokaci

Da yake magana a gefen wani taron manema labarai da ke sanar da wadanda suka lashe kyautar Zik Prize ta 2020, Utomi bai kira dandalin a matsayin jam'iyyar siyasa ba, jaridar The Nation ta ruwaito.

2023: Pat Utomi yayi magana game da rade-radin sabuwar jam'iyyar siyasa a ranar 1 ga watan Oktoba
2023: Pat Utomi yayi magana game da rade-radin sabuwar jam'iyyar siyasa a ranar 1 ga watan Oktoba Hoto: Punch
Source: UGC

Ya ce kungiyar tayi shige da sauran da ke da ra’ayi wajen samun kwararrun shugabanni a mulki, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba, Theeagleonline ta kuma ruwaitowa.

“A’a, bana tunanin (runduna ta uku) za ta zama jam’iyyar siyasa. Muna bukatar tattara wasu daga cikin wadannan kungiyoyi, mu yunkuri wajen inganta kasar,” in ji Utomi.

Baya ga Utomi, wadanda suka kafa RNP sun hada da tsohon gwamnan jihar Kwara, Ahmed Abdulfatai; tsohon ministan ilimi, Farfesa Tunde Adeniran; tsohon gwamnan jihar Cross River Donald Duke; Sanata Lee Maeba.

Sauran sune tsohon dan majalisar wakilai Usman Bugaje; tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega; Amb. Nkoyo Toyo, Yomi Awoniyi, Dr. Rose Idi Danladi da Dr. Sadiq Gombe da sauransu.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda ka iya dawowa da karfi a shekarar 2023

Kwanan baya an rahoto Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) tana cewa kwanan nan kungiyoyi 95 suka nemi a yi masu rajista a matsayin jam’iyyun siyasa.

Attahiru Jega da wasu manyan Najeriya sun kirkiri sabuwar jam'iyyar ceto Najeriya

A baya, mun ji cewa gabanin babban zaben shekarar 2023, wasu fitattun ‘yan Najeriya sun kafa runduna ta uku mai suna Rescue Nigeria Project (RNP).

Wadanda suka kafa RNP sun ce sun kaddamar da sabon tsarin siyasa ne domin baiwa 'yan Najeriya madadin jam'iyyar APC, da babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wadanda suka kafa RNP sun hada da tsohon gwamnan jihar Kwara; Ahmed Abdulfatai, tsohon dan takarar shugaban kasa, Farfesa Pat Utomi, tsohon ministan ilimi; Farfesa Tunde Adeniran da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng