Barau Ya Tuna Sadaukarwar Oluremi Tinubu, Ya Fadi Abin da Allah Ya Biya Ta da Shi

Barau Ya Tuna Sadaukarwar Oluremi Tinubu, Ya Fadi Abin da Allah Ya Biya Ta da Shi

  • Sanata Barau Jibrin ya yi magana game da sadaukarwar da matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta yi
  • Barau Jibrin ya ce Allah ya saka wa Oluremi Tinubu saboda jajircewarta a majalisar dattawa lokacin da ta ke sanata
  • Ya goyi bayan shawarar duba halartar sanatoci bayan zaman majalisa domin a karrama masu nuna jajircewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mataimakin shugaban majalisar ya bukaci sanatoci su dauki nauyin wakilcin al'umma da muhimmanci.

Barau Jibrin ya bayyana cewa sadaukarwar da Sanata Oluremi Tinubu ya taimake ta a rayuwa saboda jajircewa da ta yi.

Barau ya yabawa jajircewar Oluremi Tinubu
Sanata Barau Jibrin da matar shugaban kasa, Oluremi Tinubu. Hoto: Barau I Jibrin, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Sanata Barau ya bayyana hakan ne a zaman majalisa na ranar Talata 14 ga watan Yulin 2026, cewar TheCable.

Lokacin da Oluremi ta zauna a majalisa

Remi Tinubu ta wakilci mazabar Lagos ta Tsakiya a majalisar dattawa daga ranar 6 ga Yunin 2011 zuwa 11 ga Yunin 2023.

Kara karanta wannan

Akpabio ya kare dangantakar majalisa da Tinubu, ya fadi dalili

Bayan mijinta Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa na 2023, ta zama uwargidan shugaban kasa ta Najeriya.

Barau ya ce Allah ya saka wa Oluremi Tinubu saboda jajircewarta da kiyaye lokaci yayin da take sanatociya.

Barau ya yi wannan jawabi ne bayan Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya ya ba da shawarar a rika daukar halartar sanatoci a karshen kowane zama.

Ningi ya ce hakan zai taimaka wajen gane sanatocin da suke zama a zauren majalisa har zuwa lokacin da aka dage zaman, tare da karrama su saboda jajircewarsu.

Majiyoyi sun ruwaito cewa kafin dage zaman majalisar, sanatoci kasa da 50 ne suka rage a cikin zauren majalisar yayin da ake shirin kammala zaman.

Da yake goyon bayan shawarar, Barau ya ce shugabancin majalisa na yaba wa masu himma, sannan Allah ma yana saka wa masu gudanar da aikinsu da gaskiya.

Ya ce Oluremi Tinubu ita ce mutum ta farko da kan isa majalisar yayin da take sanatociya, kuma tana kasancewa a zauren har sai an kammala zaman.

Kara karanta wannan

'Buhari ya yi mulki irin wanda Musulunci ya nemi a yi': Alhassan Ado Doguwa

Barau Jibrin ya yaba da jajircewar Oluremi Tinubu
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin. Hoto: Barau I Jibrin.
Source: Facebook

Sakayyar da Allah ya yi wa Oluremi

Barau ya kara da cewa irin wannan jajircewa ce Allah ya saka mata da matsayin uwargidan shugaban kasa, yana mai jaddada cewa aiki tukuru yana da lada, cewar Punch.

Ya bukaci sanatoci su dauki nauyin wakiltar al'umma da muhimmanci, domin jama'a ne suka zabe su don su yi musu hidima da kuma yi wa kasa baki daya aiki.

Tun da farko, babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Tahir Monguno, ya ce ya taba samun lambar yabo saboda kiyaye lokaci lokacin da yake dan majalisar wakilai.

Monguno ya ce wannan karramawa ta taimaka masa wajen zama babban mai tsawatarwa a majalisar da ta biyo baya.

Tattaunawar ta biyo bayan shawarar Ningi ta yin koyi da majalisar wakilai wajen daukar halarta bayan zaman majalisa.

Barau ya yaba da tsarin yana sandan jihohi

Mun ba ku labarin cewa mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya yi magana kan rundunar 'yan sandan jihohi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan sandan jihohi: Barau Jibrin ya fadi amfanin shirin ga Arewacin Najeriya

Barau ya ce hakan zai ƙarfafa tsaro tare da kawo zaman lafiya mai ɗorewa musamman a Arewacin Najeriya.

Sanatan ya bayyana cewa kudirin ya samu shawarwari daga bangarori daban-daban, tare da sanya matakan kariya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.