Bayan Sauya Shekar Kwankwaso, An Samu Gwamna na Farko da Zai Koma Jam'iyyar ADC
- Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya tabbatar da shirinsa na sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar hadaka ta ADC
- Ya fadi haka ne a fadar gwamnatin Bauchi yau Talata jim kadan bayan ganawa da wakilan ADC karkashin jagorancin Babachir David Lawal
- Sanata Bala ya kuma tabbatar da cewa ya yi yunkurin shiga APC amma lamarin ya ci tura duk da zaman da ya yi da Bola Tinubu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya tabbatar da cewa ADC ce zabinsa a matsayin jam'iyyar siyasar da zai koma bayan ya bar jam'iyyar PDP.
Hakan na nuna cewa da yiwuwar Gwamna Bala ya fice daga PDP da ke fama da rikice-rikice, yayin da yan adawa ke shirin kulla hadaka mai karfi gabanin zaben 2027.

Source: Twitter
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a Bauchi ranar Talata, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Gwamnan Bauchi zai koma jam'iyyar ADC
Jim kadan bayan wata ganawar sirri da tawagar ADC karkashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, Gwamna Bala ya ce ADC ce zabinsa na gaba.
Ya ce bayan tattaunawa da shawarwari da dama, ADC ta zama jam’iyyar da ta fi dacewa da shi da abokan siyasarsa.
“Mun bar dukkan kofofinmu a bude, har da APC, amma mun gano cewa ba za mu zauna a inda ba a son mu ba. Dole ne mu nemo mafita a cikin bangaren adawa,” in ji Bala Mohammed.
Dalilin da ya sa gwamnan ya zabi ADC
Bala ya bayyana ADC a matsayin jam’iyya mai dorewa kuma mafi karbuwa ga masu ruwa da tsaki da yake tuntuba, yana mai cewa ya yi jinkirin yanke hukunci na karshe ne saboda tattaunawa da yake yi da bangarorin siyasa daban-daban.
A cewarsa:
“Saboda ina kula da muhimman bangarori biyu, Bauchi da kasa baki daya, dole ne mu yi komai yadda ya kamata.
"Dole ne mu hada kan muradun jam’iyya a matakin kasa da jiha, musamman a cikin PDP, hakan ya sa tattaunawa ta dauki lokaci.”

Source: Twitter
Gwamna Bala ya fadi dalilin rashin shiga APC
Gwamna Bala ya kuma bayyana cewa ya yi yunkurin shiga APC a baya amma bai yi nasara ba, duk da ganawar da ya yi da Shugaban Kasa Bola Tinubu da shugabannin jam’iyyar na kasa
Ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tuntubar muhimman masu ruwa da tsaki domin kauce wa kura-kurai, yana mai jaddada muhimmancin hadin kai wajen gina bangaren adawa mai karfi, cewar rahoton Punch.
“Mutanen ADC ‘yan uwanmu ne. Wasu sun shiga tun da wuri, mu kuma yanzu muke shirin shiga,” in ji shi.
Wani tsohon dan PDP da ya jima da komawa ADC a Katsina, Kabir Abdullahi Dogo ya yi maraba da wannan yayin da yake hura da wakilin Legit Hausa knlan shirin da suke na tunkarar zaben 2027.
Matashin dan siyasar ya ce sauya shekar Kwankwaso kadai ta isa ta girgiza APC kuma da izinin Allah sai ADC ta karbi kasar nan a 2027.
"Idan gwamnan Bauchi ya dawo ADC to babu abin da ya rage a PDP, shi ne shugaban gwamnonin jam'iyya, muna maraba da shi kuma wannan alama ce da ke nuna yan Najeriya sun gaji da APC," in ji shi.
NNPP ta shirya yin hadaka da ADC
A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar adawa ta NNPP ta bayyana shirin haɗin gwiwa da ADC domin a yi wa APC rubdugu a babban zaɓen 2027.
Mai magana da yawun tsagin jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin jim kadan bayan Sanata Rabiu Kwankwaso ya sauya sheka zuwa ADC.
Johnson ya ƙara da cewa an gudanar da tattaunawa mai yawa tsakanin shugabannin adawa kafin Kwankwaso ya yanke shawarar komawa ADC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


