Atiku da Kwankwaso na Tsaka Mai Wuya, Kotun Koli Ta Zo Matakin Karshe kan Rikicin ADC
- Jam'iyyar hadakar 'yan adawar Najeriya karkashin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, David Mark na dab da sanin makomarta
- Kotun kolin Najeriya ta shirya yanke hukunci kan rikicin shugabanci da ya addabi ADC tsakanin tsagin David Mark da na Nafiu Gombe
- Tsofaffin 'yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na cikin wadanda suka shiga wannan hadaka a ADC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kotun koli ta Najeriya ta shirya yanke hukunci kan karar da aka daukaka zuwa gabanta dangane da rikicin shugabancin jam'iyyar hadaka, ADC.
Kwamitin alkalai biyar karkashin jagorancin Mai shari’a Mohammed Garba ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, inda ya ce za a sanar da lauyoyin bangarorin ranar da za a yanke hukuncin.

Source: Twitter
Lauyoyi sun gabatar da hujjoji a Kotun koli

Kara karanta wannan
2027: Shugaba Tinubu ya ci gaba da sukar 'yan adawa, ya bayyana 'yaudarar' da suke yi
Rahoton Daily Trust ya ce mai shari’a Garba ya bayyana hakan ne bayan lauyoyin bangarori biyu da ke ikirarin shugabancin ADC sun gabatar da hujjojinsu tare da rokon kotu ta amince da bukatunsu.
Shugaban tsagin ADC na kasa, Sanata David Mark ne ya shigar da wannan karar mai lamba SC/CV/180/2026 gaban kotun kolin Najeriya.
Karar dai ta kalubalanci hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar 12 ga Maris, 2026, kamar yadda jaridar The Nation ta kawo.
Yadda aka faro shari’ar rikicin ADC
Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar Mark, wadda ke kalubalantar hukuncin da Mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yanke a ranar 4 ga Satumba, 2025.
A wancan hukunci, kotun ta ki amincewa da wasu bukatun umarnin gaggawa da Mark ya shigar a karar da wani jigo a jam’iyyar ADC kuma wanda ke ikirarin shugabanci, Nafiu Bala Gombe, ya shigar.
Kotun koli ta shirya raba gardama
A yanzu haka, bangarorin da abin ya shafa na jiran ranar da kotun koli za ta bayyana domin yanke hukunci kan wannan rikici na shugabanci.
Bayan sauraron kowane bangare a zaman yau Laraba, 22 ga watan Afrilun 2026, Mai shari’a Mohammed Garba, ya ce kotun koli za ta yanke hukuncinta a zama na gaba.

Source: Facebook
Ya kuma shaida wa lauyoyin bangaren David Mark da tsagin Nafi'u Gombe cewa kotun za ta sanar da su ranar da za a dawo domin jin hukuncinta na karshe.
ADC zai ita ce jam'iyyar da manyan kusoshin adawa irirnsu Atiku Abubakar, Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka kulla hadaka don kifar da gwamnatin APC a zaben 2027.
ADC shirin karbar manyan jiga-jigan siyasa
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta ce nan ba da jimawa ba za ta karbi wasu manyan 'yan siyasar Najeriya a shirye-shiryen tunkarar zaben 2027.
Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi ya ce tun farko sun tsara bin hanyoyin da suka dace don haɗakar ta ci gaba da girma, yana mai cewa ana sa ran karin manyan jiga-jigai bayan sauya shekar Kwankwaso.
Ya soki APC da hukumar zabe, INEC kan rikicin cikin gida da ADC ke fuskanta, yana mai cewa hakan ya kara masu kwarin gwiwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
