A Karon Farko, Matatar Dangote Ta Hako 'Danyen Mai a Najeriya
- Matatar mai ta Dangote ta sanar da cewa an fara samun nasarori a aikin hakar 'dan man fetur daga wasu daga cikin kadarorinsa na a Neja Delta
- Ana sa ran fara samar da danyen mai na kasuwa cikin makonni masu zuwa bayan an yi gwaje-gwaje domin tabbatar da ingancinsu
- Devakumar Edwin, mataimakin shugaban kamfanin Dangote ya bayyana cewa an samu damar fara gwajin farko na danyen man matatar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Niger Delta – Devakumar Edwin, mataimakin shugaban matatar Dangote, ta fara gwajin farko kan danyen mai daga kadarorin da yake da su a yankin Neja Delta.
Edwin ya ce kamfanin ya bude rijiyar mai guda da ya mallaka, inda aka fara gwajin da aka saba yi domin tantance ingancinsa.

Kara karanta wannan
Mataimakin gwamna ya gina sababbin masallatai 50 don taimakawa addinin musulunci a Najeriya

Source: Getty Images
Jaridar The Cable ta rahoto Devakumar Edwin ya ce ana sa ran kammala wannan gwaji cikin makonni uku zuwa hudu mafi yawa.
Matatar Dangote ta fara hako mai
Premium Times ta wallafa cewa Devakumar Edwin ya kara da cewa bayan kammala wannan mataki, za a iya fara fitar da 'danyen man da yawa, sannan kamfanin zai ci gaba da hako sababbin rijiyoyi domin kara yawan wanda za a hako.
Wannan ci gaban na nuna cewa matatar Dangote na kokarin fadada harkokinsta daga sarrafa mai kawai zuwa hako shi kai tsaye, abin da zai kara masa karfin iko a bangaren makamashi a Najeriya.
A nasa bangaren, David Bird, babban jami’in gudanarwa na matatar Dangote, ya ce wannan sabon mataki na iya samar wa matatar danyen mai mai dorewa.
Ya bayyana cewa matatar na kuma kokarin samar da jiragen ruwansa domin rage kudin jigilar mai da kuma inganta yadda ake samun danyen mai cikin sauki.

Kara karanta wannan
"Wasun su hotiho ne": Tsohon dan majalisa ya gargadi Tinubu kan dogaro da gwamnoni a 2027
Matatar Dangote za ta fadada aiki
Bird ya ce idan aka hada wannan da samarwar gida daga kamfanin WAEP, jiragen Dangote za su taimaka wajen samar da tsayayyen danyen mai ga matatar, cikin tsari mai hade daga hako mai har zuwa sarrafa shi.
Sai dai ya jaddada cewa duk da irin wannan hadin gwiwa, matatar za ta ci gaba da kula da harkokinsa cikin tsari a matakai daban-daban.

Source: Facebook
Zuwa yanzu, kamfanin tace mai na kasa, wato NNPCL ko hukumar NMDPRA ba su bayyana ra'ayinsu a kan a kan wannan sabon ci gaba da aka samu ba.
Masana na ganin cewa fara samar da danyen mai daga Dangote zai taimaka wajen rage gibin samar da mai, wanda ya taba zama babban kalubale ga matatar lokacin da ta fara aiki.
Dangote ya magantu kan Afrika
A baya, kun ji cewa attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya halarci wani muhimmin taron tattalin arziki da aka gudanar a birnin Washington DC na kasar Amurka, inda ya fito da kalubalen shiyyar Afrika.

Kara karanta wannan
Abubuwan da 'yan Najeriya za su gani idan jam'iyyar ADC ta kifar da Tinubu a zaben 2027
Dan kasuwar ya bayyana wasu abubuwan da suke hana kawo cigaba a Afrika tare da dakile tattalin arzikin kasashen yankin da dama, da suka hada da tsoma bakin wasu a kasashen waje kan harkokin yankin.
Dangote ya kuma yi magana game da muhimmancin 'yan Afrika su rika saka jari a yankunan su, domin a cewarsa hakan ne mafita a gare su da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng