Ministan Tinubu Zai Ƙara Gaba, Ya Tabbatar da Sha'awar Neman Takarar Gwamna
- Ministan wuta a gwamnatin Bola Tibubu zai nemi takarar gwamna domin bunkasa siyasarsa yayin da zabe ke kwaratowa
- Bayo Adelabu, ya fara tuntubar jiga-jigan APC a jihar Oyo domin cimma burinsa na tsayawa takarar gwamna a 2027
- Adelabu ya roki gafara daga mambobin jam’iyya da suka fusata, ya ce ba za a tilasta dan takara ba a zabe mai zuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Siyasar shekarar 2027 na cigaba da daukar zafi tun kafin fara kamfen yan takara.
Ministan Wuta, Bayo Adelabu, a ranar Juma’a ya gana da shugabannin APC da jiga-jigan jam’iyyar a Ogbomoso da Oyo a jihar Oyo.

Asali: Twitter
Ministan Tinubu ya fara shirin takarar gwamna
Yayin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar a Ogbomoso, a gidan wani jagoran jam’iyyar, Ayoade Adeseun, ministan ya ce ya fara saita hanyar siyasarsa, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wannan ganawar wani bangare ne na tuntuba kan sha'awar tsayawa takarar gwamna a jihar Oyo.
Adelabu ya ce wannan tuntuba na da nufin cimma burinsa na tsayawa takarar gwamna a 2027 a jihar Oyo karkashin jam’iyyar APC.
Yayin da yake neman goyon bayansu, Adelabu ya roki gafara daga wadanda suka fusata, yana mai cewa dole a hada kai don dawowar APC.
Ya ce:
“Na zo in sanar da ku cewa ina son tsayawa takarar gwamnan Oyo a 2027. Zan gwada kwarewata ta baya.
“Ina son in gwada abin da na koya a zabukan baya. Ba na adawa da kowane yanki. Lokacin Allah ne mafi alheri."
- Cewar Adelabu
Adelabu ya kuma bukaci al’ummar yankin su mara wa Bola Tinubu baya don sake lashe wa’adin mulki, domin cigaban yankin da kasa baki daya.
Ya kara da cewa:
“Yanzu ne lokacin Yarabawa su ci gaba da mulkin Najeriya. Idan Tinubu ya dawo, Najeriya za ta ci gaba sosai.”

Asali: Twitter
Alkawuran da Adelabu ya dauka a Oyo
A garin Oyo, Adelabu ya nemi goyon baya, yana cewa zai kafa gwamnati mai dauke da kowa da kowa, babu wanda za a bari a gefe, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce:
“Ina son mutane su gane cewa ba za a tilasta wani dan takara ba. Zan yi aiki, in tabbatar da cancanta ta.
“Oyo gida na ne na biyu. Magoya bayana da abokan tafiyata duk suna nan. Suna goyon bayana a baya kuma za su ci gaba.
“Zan ba da hakkin Oyo yadda ya kamata. Oyo yanki ne na tarihi, mai albarka da daraja a fadin jihar.”
An bukaci Tinubu ya kori ministan wuta
Mun ba ku labarin cewa matasa sun buƙaci a kori ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu da shugaban kamfanin rarraba wuta na ƙasa TCN.
Kungiyar matasan NYTGG ta ce akwai sakaci a yawan lalacewar babban layin lantarki wanda ya samu matsala sau uku a mako guda.
A cewar kungiyar, rashin wuta ya jefa ƴan Najeeiya cikin duhu, ƴan kasuwar da ke amfani da lantarki sun tafka asara mai yawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng