Gwamnatin Najeriya Ta Yi Magana kan Neman Dawo da Tallafin Man Fetur

Gwamnatin Najeriya Ta Yi Magana kan Neman Dawo da Tallafin Man Fetur

  • Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan kiran da 'yan kasa da masana ke yi na neman dawo da tallafin mai bayan tashin farashin man fetur
  • Ministan kudi, Wale Edun ya bayyana wasu matakai da ya ce gwamnatin tarayya za ta dauka domi rage radadin rayuwa ga al'umma
  • Yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a kan Iran a karshen Fabarairun 2026 ne ya jawo tsadar man fetur a duniya, ciki har da Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta bayyana cewa ba za ta dawo da tallafin man fetur ba, duk da karin farashin mai a kasuwannin duniya sakamakon tashin hankalin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

Ministan kudi, Wale Edun, ne ya bayyana hakan yayin wani taron na kungiyar G-24 da aka yi a watan Afrilun 2026 game da harkokin kudi.

Kara karanta wannan

Akwai gagarumar matsala, Iran ta sanar da asarar da ta tafka a yakin Amurka da Isra'ila

Shugaban Najeriya yayin bayani a Bayelsa
Shugaba Bola Tinubu a lokacin da ya yi bayani kan tsadar mai a Bayelsa. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Facebook

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa ya yi magana ne yayin da wasu ‘yan Najeriya ke ci gaba da kira ga gwamnati da ta dawo da tallafin mai sakamakon tsadar rayuwa da ke ƙaruwa a fadin ƙasar.

Magana kan tallafin man fetur

Wale Edun ya jaddada cewa sauye-sauyen da Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fara a 2023, ciki har da cire tallafin mai sun kasance muhimman matakai da suka samu goyon bayan cibiyoyin kudi na duniya.

Ya ce:

“Kamar yadda ku ka sani, Najeriya ta dauki mataki cikin gaggawa karkashin shugaban da ya fara mulki a 2023 wajen cire tallafin man fetur da canjin kudi.”

Ya kara da cewa duk da cewa ana fara ganin sakamako mai kyau daga wadannan gyare-gyare, wasu matsaloli daga waje sun shafi ci gaban da ake samu.

“Wadannan nasarori da ake samu cikin sauri sun gamu da kalubale daga wasu matsaloli na waje da ba su da alaka da Najeriya ko kasashe masu tasowa gaba daya,”

Kara karanta wannan

"Ba mu yarda ba," Malaman Musulunci sun tunkari gwamna kan 'tsarin' da ya kawo a Najeriya

Inji shi.

Me za a yi a madadin maido tallafi?

Nairametrics ta wallafa cewa Edun ya ce abin da ya kamata a maida hankali a kai shi ne tallafawa masu karamin karfi ta hanyoyi na musamman, maimakon janye gyare-gyaren da ake yi.

A cewarsa, duk da cewa kasashe masu arzikin mai kamar Najeriya na iya samun karin kudin shiga sakamakon tashin farashin mai, akwai kuma kalubale saboda karin farashin makamashi na iya janyo karin kudin taki da abinci.

“Karin farashin makamashi yana shafar fannoni da dama kamar taki da abinci,”

In ji Edun.

Wale Edun tare da shugaba Bola Tinubu
Wale Edun ya mikawa Bola Tinubu wani rahoto a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Edun ya kara da cewa dole ne gwamnatoci su tinkarar irin wadannan matsaloli, tare da tabbatar da cewa duk wani tallafi da za a bayar ya kasance na wucin gadi kuma ya fi karkata ga talakawa da masu bukata.

Maganar Tinubu kan tsadar mai

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yi magana game da tsadar man fetur da ake fama da ita a Najeriya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Matsalar da aka samu a sulhun Amurka da Iran ya rusa burin 'yan Najeriya

Tinubu ya tabbatar da cewa ana wahala amma kuma lamarin na da sauki idan aka kwatanta da halin da ake ciki a Kenya da wasu kasashe.

Shugaban kasar ya bayyana cewa duk da haka zai cigaba da daukar matakai masu muhimmanci domin kawo saukin rayuwa ga 'yan kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng