"Tinubu na Yi wa Dimokuradiyya Shakar Mutuwa": Obi Ya ce da Matsala a gabanin 2027
- Tsohon 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da takura wa jam’iyyun adawa a kasar nan
- Ya bayyana zargin cewa gwamnatin ta nemi a hana su dakin taron jam'iyyar hamayya ta ADC, wanda ke nuna shake jam'iyyar hamayya ta kasa
- Mista Peter Obi, ya gargadin cewa tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya na fuskantar barazana yayin da ake shirin babban zaɓen 2027 da zai dauki hankalin duniya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da takura wa harkokin siyasar adawa a Najeriya.
Ya bayyana cewa wannan abu da gwamnatin ke yi masu ya nuna karara cewa ana kokarin shake dimokuraɗiyyar Najeriya da tauye hakkin 'yan adawa.

Source: Facebook
Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi Arise TV, inda ya nuna damuwa kan yadda aka hana jam’iyyarsa ta ADC, samun manyan wuraren taro a Abuja domin gudanar da babban taronta na ƙasa.
Obi ya koka kan dimokuradiyyar Najeriya
Jaridar Leadership ta ruwaito a cewar Peter Obi, wannan mataki alama ce ta koma baya a harkar dimokuraɗiyya a kasar nan.
Ya ce:
“Idan aka hana ku abubuwa masu sauƙi kamar wurin taro, hakan na nuna inda ƙasa ke nufa."

Source: Twitter
Ya ƙara da cewa tsarin mulkin Najeriya ya tanadi ‘yancin haɗuwa da gudanar da siyasa, amma abin takaici jam’iyyar adawa ba ta samun damar yin aiki yadda ya kamata.
Obi ya zargi gwamnati da rashin bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya, yana mai cewa akwai wani yunƙuri na rage ƙarfin jam’iyyun adawa ko ma danne su gaba ɗaya.
Obi ya magantu kan taron ADC
Duk da waɗannan ƙalubale, Obi ya jaddada cewa taron jam’iyyar ADC zai gudana kamar yadda aka tsara ba tare da an samu wata babbar matsala ba.
Ya ce:
“Za a yi taron, kuma zan halarta.”
Obi ya kuma soki INEC musamman kan janye amincewa da wani ɓangare na shugabancin jam’iyyar da David Mark ke jagoranta.
Ya ce matakin ya haifar da tambayoyi, domin a baya an amince da irin wannan shugabanci. Hakan, a cewarsa, na nuna rashin daidaito a cikin tsarin gudanar da zaɓe.
Har ila yau, Obi ya nuna damuwa cewa cibiyoyin dimokuraɗiyya kamar bangaren shari’a na ƙara shiga cikin rikice-rikicen siyasa, lamarin da ya ce na rage amincewar jama’a da tsarin gaba ɗaya.
Obi ya magantu kan Arewa
A baya, mun wallafa cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, Peter Obi, ya yi tsokaci kan shirin da yake da shi kan yankin Arewacin Najeriya idan ya samu dama.
Peter Obi ya bayyana cewa yana da shirin ganin ya kawo ci gaba mai yawa a Arewa saboda muhimmancin da yankin yake da shi ta fuskoki daban-daban da suka hada da ci gaban tattalin arziki.
Hakazalika, Peter Obi ya kuma yi magana kan hanyoyin da ya kamata a bi domin magance matsalar rashin tsaron da ake fama da ita, wacce ta hana jama'ar yankin sukuni da zama lafiya.
Asali: Legit.ng


