Siyasa Ta Ɗauki Zafi: Ƴan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice daga Jam'iyyar PDP zuwa APC

Siyasa Ta Ɗauki Zafi: Ƴan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice daga Jam'iyyar PDP zuwa APC

  • Tajudeen Abbas ya karanto wasikun wasu ‘yan majalisar wakilai uku daga Kaduna, na sauya shekarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC
  • Gwamna Uba Sani ya halarci zaman majalisar don marabtar ‘yan majalisar zuwa APC, lamarin da ya nuna tasirinsu a siyasar Kaduna
  • Sauya shekar 'yan majalisar ya raunana PDP a Kaduna, yayin da APC ke kara karfi a majalisar wakilai da kuma Arewa maso Yamma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya karanta wasikun sauya shekar wasu ‘yan majalisa uku daga jihar Kaduna zuwa jam’iyyar APC.

An sanar da hakan ne a zaman majalisar na ranar Talata, inda aka bai wa Gwamnan Kaduna, Uba Sani, damar halartar zaman domin yin maraba da sababbin ‘ya’yan APC.

'Yan majalisar wakilai 3 daga Kaduna sun sauya sheka daga PDP zuwa APC
Zauren majalisar wakilai yayin da ake zaman majalisar karkashin Abbas Tajudeen. Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

'Yan majalisar Kaduna sun bar PDP zuwa APC

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Gwamna ya bayyana bullar sabuwa kungiyar ta'addanci a yankinsa

Rahoton jaridar Premium Times ya nuna cewa ‘yan majalisar wakilan Kaduna da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC sun haɗa da:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

  • Hon. Hussaini Ahmed (mai wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu),
  • Hon. Aliyu Abdullahi (mai wakiltar mazabar Ikara/Kubau), da
  • Hon. Sadiq Abdullahi (mai wakiltar mazabar Sabon Gari).

An rahoto cewa sauya shekar 'yan majalisar wakilan ya sake raunana karfin PDP a majalisar da kuma jihar Kaduna, tun bayan zaben 2023.

Wannan sauya shekar, ya kusan jawo ce-ce-ku-ce a majalisar daga bangaren marasa rinjaye, wadanda suka bukaci a wofantar da kujerar wakilan uku.

Dalilin 'yan majalisar 3 na sauya sheka

Yayin da yake bayyana dalilinsa na sauya sheka, Hon. Hussaini Ahmed ya ce sauya shekar ne bayan “tattaunawa mai fadi da al’ummarsa da shugabannin siyasa.”

A cewarsa, sai da al'ummarsa da shugabannin siyasar suka yarda cewa haɗin kai da jam’iyya mai mulki zai kawo ci gaba ga mazabarsu, sannan ya sauya sheka.

“Mun tattauna sosai da jama’ata. Mun fahimci cewa idan muka haɗa kai da gwamnati mai mulki, za mu iya kawo ayyukan raya kasa da dama.”

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gano maɓuyar hatsabibin ɗan bindiga, Mai Duna, an yi musayar wuta

- Hon. Hussaini Ahmed.

Hon. Aliyu Abdullahi daga Ikara/Kubau ya ce sauya shekar tasa wani bangare ne na ƙarfafa matsayinsa na siyasa yayin da ake shirye-shiryen tunkarar zabukan gaba, inji rahoton Vanguard.

Uba Sani ya halarci zaman majalisar wakilai inda 'yan majalisar Kaduna 3 suka koma APC daga PDP
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani yana jawabi a wani taro da aka gudanar a Kaduna. Hoto: @Ubasanius
Source: Facebook

PDP ta kara rage tasiri a Kaduna

Shi kuma Hon. Sadiq Ango Abdullahi na Sabon Gari, wanda ake ganin matashi ne a siyasa, ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin “ƙarfafa tasirinsa a cikin jam’iyyar da ke da rinjaye a jihar.”

Rahotanni sun nuna cewa sauya shekar ta kara raunana PDP a majalisar tarayya, musamman daga Jihar Kaduna, inda APC ke kara daidaita karfinta a matakin jiha da kasa baki daya.

Masu sharhi sun ce lamarin ya kara tabbatar da canjin da ake samu a siyasar Kaduna, inda yanzu manyan ‘yan siyasa suka nuna gamsuwa da jagorancin Gwamna Uba Sani.

'Yan majalisa 2 sun sauya sheka zuwa APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan majalisar wakilan tarayya biyu daga Kaduna da Neja sun sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

APC ta kara ba PDP rata a majalisa yayin da sanata ya koma jam'iyyar

Hon. Hussaini Mohammed Jallo, mai wakiltar Igabi da Hon. Adamu Tanko mai wakiltar Gurara/Suleja/Tafa su ne suka sanar da sauya sheka.

Shugaban majalisar wakilan, Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙun sauya sheƙar mambobin guda biyu a zaman majalisar da ya jagoranta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com