APC Ta Samu Karuwa, Ƴan Majalisar Tarayya 2 daga Kaduna da Neja Sun Fice daga PDP
- Ƴan Majalisar Wakilan Tarayya biyu daga jihohin Kaduna da Neja sun sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai rinjaye
- Hon. Hussaini Mohammed Jallo, mai wakiltar Igabi da Hon. Adamu Tanko mai wakiltar Gurara/Suleja/Tafa sun sanar da sauya-sheka
- Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya, Tajudeen Abbas ya karanta wasiƙun sauya sheƙar mambobin guda biyu a zamansu na yau a Abuja
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ƴan Majalisar wakilan tarayya biyu sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a zamansu na yau Talata, 18 ga watan Maris, 2025.
Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ne ya karanta wasikun da ƴan Majalisar suka rubuto domin tabbatar da komawarsu jam'iyyar APC.

Asali: Facebook
Hakan na kunshe ne a wani faifan bidiyo da Imran Muhammad, wani mai amfani da kafar sada zumunta ya wallafa a shafinsa na X watau Tuwita.

Kara karanta wannan
Wike ya soke takardun filaye kusan 5000, an fadi sharadin mayar wa jama'a dukiyarsu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan Majalisar Wakilai 2 sun koma APC
Waɗanda suka sauya shekar sun haɗa da Hon. Hussaini Mohammed Jallo, mamba mai wakiltar mazaɓar Ugabi ta jihar Kaduna.
Sai kuma Hon. Adamu Tanko, mamba mai wakiltar mazaɓar Gurara/Suleja/Tafa ta jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
Hon. Jallo Hussaini da Hon. Adamu Tanko, sun mika wasikun murabus dinsu daga PDP, tare da sanar da sauya sheƙa zuwa APC a hukumance a zaman Majalisa na yau Talata.
Sauya shekar wadannan ‘yan majalisa ya kara rage karfin jam’iyyar PDP a majalisar wakilai yayin da ita kuma APC ta samu ƙaruwar mambobinta.
Kakakin Majalisa ya taya su murna
Wannan mataki na iya tasiri a siyasar majalisar, musamman a bangaren yanke manyan hukunci da zartar da kudurori masu muhimmanci.
Da yake karanta wasikar ɗan Majalisar mai wakiltar Igabi, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya taya masu sauya sheƙar murna tare da yi masu maraba da zuwa jam'iyya mafi girma a Afirka.
"Ina maku maraba zuwa jam'iyya mafi girma a Afirka, jam'iyyar kawo sauyi da ci gaban ƙasa," in ji Tajudeen Abbas.
Me ya sa ƴan Majalisar suka koma APC
A wasiƙar sauya shekarsa, Hon. Hussaini Mohammed ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa APC ne saboda rikicin da ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa a PDP.
Hussaini, wanda shi ne dan majalisa na biyu a PDP daga jihar Kaduna da ya koma APC, ya ce kalubalen da ake fuskanta a jam’iyyar ya yi tsananin da ba zai iya ci gaba da zama ba.

Asali: Facebook
A nasa ɓangaren, Hon. Adamu Tanko ya ce ya tuntubi jama’ar mazabarsa tare da yanke shawarar sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai, Hon. Kingsley Chinda ya yi fatali da sauya shekar ƴan Majalisar, ya ce ƴan adawa ba za su gaji da nuna ɓacin ransu ba sai an yi abin da ya dace.

Kara karanta wannan
A karon farko, jam'iyyar APC ta kasa ta yi maganar sauya shekar El Rufai zuwa SDP
APC na shirin ba Tinubu tikitin tazarce
A wani labarin, kun ji cewa alamu sun nuna cewa APC na shirin ɓa shugaban kasa, Bola Tinubu da mafi yawan ƴan Majalisunta tikitin neman tazarce a zaɓen 2027.
Majiyoyi dama daga cikin APC sun tabbatar da hakan, suj ce galibin masu faɗa a ji na jam'iyyar sun amince da wannan mataki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng