APC Ta Kara ba PDP Rata a Majalisa yayin da Sanata Ya Koma Jam'iyyar

APC Ta Kara ba PDP Rata a Majalisa yayin da Sanata Ya Koma Jam'iyyar

  • Jam'iyyar APC mai mulki da kuma rinjaye a majalisun Najeriya ta kara yawan sanatocin da ta ke da su a majalisar dattawa
  • Hakan na zuwa ne bayan sanatan Bauchi ta Arewa, Samaila Dahuwa Kaila ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC
  • Sanata Dahuwa Kaila ya yi bayanin abubuwan da suka ja hankalinsa ya bar PDP wadda ya lashe zabe a karkashinta a shekarar 2023

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa, Dr. Samaila Dahuwa Kaila, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Sanata Samaila Dahuwa Kaila ya koma jam'iyyar APC mai mulki ne bayan ya yi murabus daga PDP.

Sanata Samaila Dahuwa Kaila ya koma APC
Sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa, Samaila Dahuwa Kaila. Hoto: Hassan Shehu Reyes
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya karanta takardar sauya shekarsa a ranar Talata, 14 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan

Siyasa ta dauki zafi: Ƴan majalisar tarayya 3 sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Godswill Akpabio ya karanta wasikar sauya shekar Sanata Samaila Dahuwa Kaila zuwa APC ne a zauren majalisar dattawa.

Sanata Samaila Dahuwa Kaila ya fice daga PDP

Sanata Samaila Dahuwa Kaila ya bayyana cewa ya bar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar a matakai daban-daban.

A cikin wasikar, Sanata Samaila Dahuwa Kaila ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyar PDP ne suka tilasta masa yanke wannan shawara.

A cewarsa, wadannan matsalolin sun takaita masa damar yin aiki da gaskiya da kuma kula da muradun mazabarsa yadda ya kamata, rahoton jaridar Vanguard ya zo da labarin.

"Rikice-rikicen da suka dabaibaye jam’iyyar PDP sun hana ni yin aikina na majalisa cikin gaskiya da kwanciyar hankali"
"A matsayina na wanda ke da cikakken kishin kasa da kuma jin dadin al’ummata, na ga dacewar na daidaita al’amurana da wata jam’iyya mai hangen nesa wacce take wakiltar nagartaccen mulki, hadin kai, ci gaba da tsari mai kyau a cikin tafiyar kasar nan.”

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Tsohuwar minista a Najeriya ta yi bankwana da duniya

- Sanata Samaila Dahuwa Kaila

Me yasa Sanatan Bauchi ya koma APC?

Sanatan ya ce shigowarsa jam’iyyar APC ta samo asali ne daga girmamawa da goyon bayansa ga manufofin sauyi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa a halin yanzu.

Samaila Dahuwa Kaila ya koma jam'iyyar APC
Sanata Samaila Dahuwa Kaila a zauren majalisar dattawa. Hoto: Hassan Shehu Reyes
Source: Facebook
"Saboda haka, na zabi shiga jam’iyyar APC domin na bada cikakken goyon baya ga sauye-sauyen shugabanci da Mai girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ke jagoranta."
"Ina matukar girmama wadannan matakai masu karfin hali da ke nufin dawo da daidaiton tattalin arziki, karfafa tsarin mulki, da kuma gyaran kasar nan domin dorewar cigaba.”

- Sanata Samaila Dahuwa Kaila

Da wannan sabon ci gaban, yawan kujerun Sanatoci a majalisar dattawa yanzu ya zama kamar haka, APC – 74, PDP – 27, LP – 4, APGA – 2, NNPP – 1, SDP – 1.

Gwamnan Enugu ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Enugu, Peter Ndubuisi Mbah ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: An ji dalilin da ya sa gwamnan PDP ya sauya sheka zuwa APC

Gwamnan Peter Mbah ya sanar da komawarsa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, a hukumance a ranar Talata, 14 ga watan Oktoban 2027.

Peter Mbah ya bayyana cewa ya dauki dogon lokaci yana nazari kafin daga bisani ya yanke shawarar komawa jam'iyyar APC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng