'Yan Sanda Sun Gano Maɓuyar Hatsabibin Ɗan Bindiga, Mai Duna, an Yi Musayar Wuta
- ‘Yan sanda sun yi nasarar dakile shirin garkuwa da mutane a dajin Abuja, sun kwato makamai bayan fafatawa da miyagu
- Kwamishinan ‘yan sanda ne da kansa ya jagoranci fafatawa da 'yan ta'addar, a shirin dakile barazanar tsaro a birnin tarayya
- Rundunar 'yan sandan ta lissafa yankuna uku da ta karfafa sintirin jami'anta, inda kuma ta nemi hadin kan mazauna garin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rundunar ‘yan sanda ta babban birnin tarayya (FCT) ta samu nasarar hana wani mummunan shirin garkuwa da mutane a Abuja.
An ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga ne suka shirya kai harin garkuwa da mutane a dajin Byazhin, wanda ke kusa da yankin Kubwa a Abuja.

Source: Twitter
An gano mafakar ‘yan bindiga a Abuja
Jaridar Leadership ta rahoto cewa 'yan sanda sun kai samamen gaggawa dajin a cikin dare, inda suka tarwatsa ‘yan bindigar kafin su kai hari ga al’umma.

Kara karanta wannan
Atiku da fitattun 'yan Najeriya, kungiyoyi da jam'iyyu da suka yi adawa da afuwar Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin rundunar 'yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.
Ta ce jami’an 'yan sandan sun gudanar da bincike a cikin dajin Byazhin, inda suka gano wurin da ‘yan bindigar suke buya tare da kwato makamai da alburusai.
“An kwato bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, alburusai 30, da wasu kayan sadarwa da suka nuna shirin kai hari."
- SP Josephine Adeh.
Dabar Mai Duna ta shirya kai hari
A cikin sanarwar, rundunar ta ce sashen fikirarta ya gano cewa kasurgumin dan ta'adda, Mai Duna ya gama shiri na kai hare-hare a wasu kauyukan da ke kusa da dajin Byazhin.
"Bisa bayanan sirri, sashen yaki da garkuwa da mutane na rundunar ya kai samame dajin, inda ya yi wa 'yan ta'addar kwanton bauna.
"Da misalin karfe 1:00 na safiyar ranar 11 ga Oktoba, 2025, jami'an 'yan sanda suka yi artabu da tawaga biyu ta 'yan ta'adda da ke shirin kai hari, inda aka yi musayar wuta ta kusan mintuna 20."

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi artabu da 'yan ta'adda ana batun sulhu a Katsina, mutum 12 sun kwanta dama
- SP Josephine Adeh.

Source: Twitter
’Yan sanda sun kara sintiri a Abuja
Punch ta rahoto kwamishinan ‘yan sanda na Abuja, CP Benneth Igweh, ya bayyana cewa wannan nasara alama ce ta sabuwar dabarar tsaro da rundunar ke amfani da ita don kare rayuka da dukiyar al’umma.
“Ba za mu lamunci barazanar tsaro a Abuja ba. Rundunar za ta ci gaba da kai samame a duk dazuzzukan da ke a cikin birnin tarayyar nan."
- CP Benneth Igweh.
Ya kuma umarci dukkan shugabannin ofisoshin 'yan sanda (DPOs) da sassan tsaron rundunar da su kara karfafa huldar da jama'a domin samun bayanai cikin lokaci.
Rahotanni sun ce an kara tsaurara tsaro a yankunan Bwari, Gwagwalada da Kuje, bayan samun labarin yuwuwar kai hare-hare a wuraren.
'Yan bindiga sun sace sarki a Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun sace Hakimin Dnako, HRH Etsu Yuda Garba, da jikokinsa biyu a birnin tarayya Abuja.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa 'yan ta'addar sun sace wasu mutum biyar daga gidaje daban-daban a cikin dare yayin harin.
Mutanen yankin sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi harbi a yankin domin tsoratar da mutane kafin su samu damar tserewa daga wajen.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
