Murna Ta Ɓarke a Majalisar Tarayya da Mambobi 2 Suka Ƙara Kassara PDP, LP a Najeriya
- Ƴan Majalisar Wakilai biyu daga Enugu da Kuros Riba sum sauya sheka daga PDP da LP, zuwa APC mai mulki a hukumance
- Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙun sauya sheƙar ƴan Majalisar a zaman yau Talata a Abuja
- Wannan sauya sheƙa dai ta yi wa ƴan APC daɗi, nan take suka ɓarke da murna da shewa, suna masu yi wa abokan aikinsu maraba da zuwa APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta samu ƙaruwa a Majalisar Wakiali ta Ƙasa a daidai lokacin da ƴan adawa ke shirye-shiryen kafa sabuwar jam'iyyar siyasa.
Mambobi biyu a Majalisar Wakilai, waɗanda suka fito daga jihohim Enugu da Kuros Riba sun sanar da sauya sheƙa a hukumance zuwa APC yau Talata.

Asali: Twitter
Ƴan majalisa 2 sun ƙara kassara PDP, LP
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wadanda suka sauya sheƙar sun haɗa da, Hon. Peter Akpanke, mai wakiltar mazabar Obanliku/Obudu/Bekwara a Jihar Cross River.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai kuma Hon. Paul Nnamchi, mai wakiltar mazabar Enugu ta Gabas/Isi Uzo a Jihar Enugu, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Hon. Peter Akpanke ya fice daga PDP zuwa APC yayin da Hon. Paul Nnamchi ya baro jam'iyyar LP domin haɗewa da jam'iyya mai mulkin Najeriya.
Dukkansu sun bayyana sauya sheƙar su ne a hukumance yayin zaman majalisar wakilai na yau Talata, 25 ga watan Yuni, 2025.
Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya karanta wasikun sauya sheƙarsu a zauren majalisa.
Meyasa ƴan Majalisa 2 suka koma APC?
A cikin wasikun da suka gabatar, ‘yan majalisar biyu sun bayyana cewa sun fice daga jam’iyyunsu ne sakamakon rikicin cikin gida da rashin daidaito a cikin PDP da LP.
Hon. Peter Akpanke, wanda aka zaɓa a karkashin tutar PDP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta gaza magance matsalolin cikin gida da ke hana ta gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Ya ce sauya sheƙar sa zuwa APC zai ba shi damar ci gaba da wakiltar al’ummarsa yadda ya dace, ba tare da shinge na rikicin cikin gida ba.

Asali: Facebook
Murna ta ɓarke ɓayan sauya shekar mambobi 2
Haka zalika, Hon. Paul Nnamchi daga LP, ya koka da cewa jam’iyyarsa ta kasa samar da cikakkiyar mafita ga matsalolin da ke tattare da jagoranci.
Ya ce yana fatan samun damar bada gudunmawa ga ci gaban Najeriya ta hanyar hadaka da jam’iyyar da ke rike da madafun iko a yanzu.
Bayan sanarwar sauya sheƙar, ‘yan majalisar jam’iyyar APC sun tafa da shewa da farin ciki, tare da maraba da sababbin mambobin jam'iyyarsu.
Ɗan Majalisa da magoya baya 10,000 sun koma APC
A wani labarin, kun ji cewa ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Udi/Ezeagu, Hon Sunday Umeha tare da manyan ƙusoshin LP sun sauya sheƙa zuwa APC.
Daga cikin jagororin LP da suka koma APC a Enugu har da tsohon ɗan Majalisar wakilai da magoya bayan LP akalla 10,000.
Hon. Umeha ya bayyana cewa yankoma APC ne ba don komai ba sai don samun damar goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng