A Yi Hattara: NNPCL Ya Fitar da Gaskiya kan Zargin Gwanjon Kayan Matatun Najeriya
- Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya yi bayani game da rahotannin da ke cewa an fara sayar da ƙarafa da sauran tarkacen matatun Najeriya
- Kamfanin ya ce akwai alamu ƴan damfara na shirin zaluntar bayin Allah da sunan NNPCL wajen sayar masu da kaya
- NNPCL ya bukaci a rika kai rahoto ga hukumomin tsaro idan an gamu da irin wadannan mutane da ke shiga rigar kamfanin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, ya yi kira ga jama’a da su yi hattara da wasu bayanai da ke yawo, wadanda ke ikirarin cewa yana sayar da tarkacen matatun mai da wasu kayan aiki ga mutane ko kamfanoni masu zaman kansu.
Wannan gargaɗi na kunshe a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Andy Odeh, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a, 24 ga watan Afrilu na shekarar 2026.

Kara karanta wannan
Ningi: Babban kuskuren da zai hana wasu sanatoci da 'yan majalisu koma wa kujerunsu a 2027

Source: Getty Images
Punch ta wallafa cewa kamfanin ya bayyana cewa bai fitar da wata sanarwar neman neman masu zuba jari ba dangane da sayar da ƙarafa ko wasu kayan aiki daga matatun mai na Fatakwal, Warri da Kaduna.
NNPCL ya magantu kan sayar da kayan matatu
NNPCL ya jaddada cewa duk bayanan da ake yadawa game da sayar da tarkacen karafa ko kayan aiki na matatun mai karya ne kamar yadda bayani ya zo a jaridar Vanguard.
A cewar sanarwar:
“NNPCL na sanar da jama’a cewa akwai wasu bayanai marasa tushe da ke cewa kamfanin yana sayar da tarkacen kayan aiki daga matatun mai ga mutane da kamfanoni masu zaman kansu.”
Kamfanin ya kara da cewa bai amince da sayar da wani abu daga rumbunan ajiya ko kayan aikin matatun kasar nan da ke jihohin Kaduna da Fatakwal ba.
Kamfanin NNPCL ya yi gargadi game da damfara

Kara karanta wannan
Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100
Kamfanin NNPCL ya kuma bayyana cewa ya samu rahotanni kan wasu mutane da ke kiran kansu wakilai ko jami’ansa, suna ikirarin cewa suna sayar da tarkacen karafa da wasu kaya da sunansa.
Ya yi gargadi cewa wadannan mutane ba su da wata alaka da kamfanin, kuma suna kokarin yaudarar jama’a ne kawai.
Saboda haka, NNPCL ya bukaci jama’a, kamfanoni da masu ruwa da tsaki a harkar mai da su yi watsi da irin wadannan bayanai.

Source: Twitter
Kamfanin ya kara da cewa duk wani sahihin bayani na sayar da kadarori zai bi tsari, tare da sanar da jama’a ta hanyoyin sadarwa na hukuma, kuma a karkashin dokoki da ka’idoji.
Har ila yau, ya bukaci duk wanda ya gamu da irin wadannan masu ikirari da ya kai rahoto ga hukumomin tsaro domin daukar mataki.
NNPCL ya sake jaddada kudirinsa na tabbatar da gaskiya, rikon amana da kuma kula da kadarorin makamashin kasa yadda ya dace.
Abin da ya faru da matatun Najeriya – NNPCL
A baya, mun wallafa cewa Shugaban kamfanin mai na kasa, Bayo Ojulari ha bayyana dalilan da suka jawo gwamnati ta rufe matatun man da ake da su.

Kara karanta wannan
"Kada ku bar Turawa su yaudare ku": Gumi ya shawarci gwamnati kan sulhu da ƴan ta'adda
Gwamnatin Najeriya dai ta dakatar da ayyukan matatun mai da suke karkashinta saboda tarin asara da ake yi duk da kuɗin da aka zuba wajen farfaɗo da su.
Shugaban kamfanin, Bayo Ojulari ya kara da cewa wannan ya sa NNPCL ya fara sauya salo zuwa kasuwanci don a samu riba, amma ba don kawai a wadata kasa da fetur.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng