Yobe: Hadimin Gwamna Ya Yi Murabus, Ya Faɗi Dalilansa na Shiga Jam'iyyar ADC
- Wani hadimin gwamnan jihar Yobe ya yi murabus daga mukaminsa inda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC da aka ƙaddamar saboda hadaka
- Matashin Babagana Yakubu Mohammed wanda hadimi ne na musamman ga Mai Mala Buni ya yi murabus daga APC
- Ya bayyana cewa ya gaji da yadda aka bar magoya bayan APC na ƙasa ba tare da karramawa ko daraja ba duk da sadaukarwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Damaturu, Yobe - Jam'iyyar APC a Yobe ta yi babban rashi bayan murabus din wani hadimi na musamman ga gwamnan jihar.
Hon. Babagana Yakubu Mohammed, mai ba Gwamnan Yobe Hon. Mai Mala Buni shawara ta musamman ya koma jam’iyyar ADC.

Asali: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da Hon. Babagana ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Asabar 6 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda APC ke rasa jiga-jiganta zuwa ADC
Wannan murabus din na zuwa ne yayin da aka ƙaddamar da jam'iyyar ADC domin kwace mulkin Bola Tinubu a zaben 2027 da ke tafe.
Jiga-jigan APC da dama sun sauya sheka zuwa jam'iyyar ta ADC domin kalubalantar shugaban da suka ce ya gallazawa mutane.
Daga cikin wadanda suka bar APC akwai tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da na Shari'a, Abubakar Malami.
Babagana ya nuna bacin ransa kan gwamnati
Babagana, wanda ya fito daga karamar hukumar Gaidam a jihar Yobe, ya sanar da murabus dinsa cikin wata wasika zuwa Sakataren Gwamnati Baba Malam Wali.
A cikin wasikar, Babagana ya nuna bacin ransa da yadda aka watsar da magoya bayan ƙasa masu jajircewa.
Ya ce:
“Ku karɓi wannan a matsayin murabus na daga matsayin Mai Ba Gwamna Shawara ta Musamman, wanda ya fara aiki nan take.
“Ina ganin an yi watsi da kokarina da gudunmawata ga jam’iyya a matakin ƙasa. Duk da biyayya ta, an ware ni.
“Ina ba da hakuri bisa irin lokacin wannan sanarwar, amma saboda wasu dalilai, na yanke shawarar yin murabus.”

Asali: Facebook
Musabbabin murabus din hadimin gwamnan Yobe
Yakubu ya bayyana murabus dinsa a matsayin daukar mataki mai wahalar yankewa amma dole ne.
“Ina da imani da akidar jam’iyyar mu, amma abin takaici ne ganin gazawar gwamnati wajen cika alkawari."
- Cewar Babagana
Babagana ya kuma zargi gwamnatin APC ta jihar Yobe da gazawa wajen duba bukatun jama’a da kuma rashin hangen nesa da tafiya da zamani.
Ya gode wa Gwamna Buni bisa damar da ya samu na yi masa aiki, tare da masa fatan alheri yayin da yake jan ragamar jihar.
Hadimin gwamnan Plateau ya yi murabus
Mun ba ku labarin cewa wani jigo a gwamnatin Plateau ya yi murabus daga mukamin mai ba gwamnan jihar, Caleb Mutfwang shawara kan harkokin siyasa.
Letep Dabang ya ajiye mukaminsa a hukumance ranar 30 ga Yuni, 2025 inda ya tabbatar da komawa jam'iyyar APC.
Dabang ya bayyana godiyarsa ga damar da aka ba shi ya yi aiki da gwamnati, kuma ya ce yana fatan gwamnati za ta ci gaba da samun nasara.
Asali: Legit.ng