'Kofarmu a Buɗe Take': Jam'iyyar ADC Ta Tura Goron Gayyata ga Dauda Lawal
- Shugaban jam’iyyar ADC a Zamfara, Kabiru Garba, ya gayyaci Gwamna Dauda Lawal da ya sauya sheka zuwa jam’iyyarsu domin ci gaban jiha
- Garba ya bayyana cewa fiye da mutum 100 daga jam’iyyu daban-daban sun shiga ADC, inda suka fara samun horo kan tsarin mulkin jam’iyyar
- Ya ce kofa a bude take ga duk masu sauya sheka, kuma za a ba kowane dan jam’iyya daidaito da dama cikin dimokuradiyya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Jam'iyyar ADC a jihar Zamfara ta tura sako na musamman ga Gwamna Dauda Lawal Dare kan zaben 2027.
Shugaban jam’iyyar ADC a jihar, Kabiru Garba, ya tura goron gayyata ga Gwamna Dauda Lawal da ya shiga jam’iyyar.

Asali: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da ya fitar yayin taron manema labarai da ya gudana a Gusau ranar Juma’a, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matawalle ya gayyaci Dauda Lawal zuwa APC
Wannan ba shi ne karon farko ba da jam'iyyu ke bukatar Dauda Lawal ya watsar da jam'iyyarsa ta PDP zuwa cikinsu a Najeriya.
Ko a kwanakin baya, tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya yi wa Dauda Lawal tayin shiga APC domin kawo cigaba a jihar.
Ya ce jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya babu abin da ta sanya a gaba sai kaddamar da ayyukan alheri ga al'umma.

Asali: Twitter
ADC ta gayyaci Dauda Lawal zuwa cikinta
Shugaban ADC a Zamfara ya ce fiye da ’yan siyasa 100 sun shiga jam’iyyar wanda ya kara tabbatar da karfinta kafin zaben 2027.
Ya ce sun tura goron gayyatar ne ga Dauda Lawal domin kokarin kawo cigaba a jihar.
Ya ce:
“Muna so mu aika da gayyata a hukumance ga Gwamna Dauda Lawal da ya shiga jam’iyyar domin kawo ci gaba a jihar.
“Kofarmu a bude take ga duk masu sauya sheka ba tare da la’akari da matsayinsu ba. Za mu ba kowa daidaito da dama.”
ADC ta samu gagarumar nasarar a Zamfara
Garba ya danganta shawarar wasu jiga-jigan siyasa a jihar da suka shiga ADC da irin jagoranci na adalci da daidaito na shugabannin jam’iyyar, cewar rahoton The Guardian.
“Muna da fiye da ’yan siyasa 100 daga jam’iyyu daban-daban, kuma muna basu horo kan tsarin jam’iyyar domin fahimtar aikace-aikacen siyasa.
“Duk masu niyyar sauya sheka su fara ne daga matakin mazaba, zuwa karamar hukuma, sannan jiha har zuwa matakin tarayya.
“Muna da yakinin siyasar tushe ce hanya mafi kyau domin bayyana amincewar jama’a bisa kuri’arsu."
- Cewar shugaban jam'iyyar
Gwamna Dauda ya magantu kan rikicin PDP
Kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi magana kan rikicin da ya daɗe yana addabar jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Dauda Lawal ya bayyana cewa rikicin na PDP ya wuce batun a ce matsala ce ta mutum ɗaya, sai dai girman kai da ya yi wa mambobin katutu.
Gwamnan ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa za a warware rikicin domin suna ƙoƙarin ganin an cimma hakan.
Asali: Legit.ng