Haɗaka: Bayan Ficewar Malami, Ministan Buhari, Amaechi Ya Watsar da jam'iyyar APC

Haɗaka: Bayan Ficewar Malami, Ministan Buhari, Amaechi Ya Watsar da jam'iyyar APC

  • Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya fice daga APC yana cewa Najeriya ta lalace gaba ɗaya, kuma al'umma ba su iya cin abinci
  • Amaechi ya zargi APC da INEC da haɗin gwiwa wajen kokarin magudin zaɓe, ya ce gwamnatin Bola Tinubu ba ta da tunani kan halin da mutane ke ciki
  • Ya ce bai taɓa yarda Tinubu ya dace da shugabanci ba, yanzu mutane na roƙon dawowar Muhammadu Buhari saboda rayuwa ta fi sauƙi a lokacinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sufuri, Rt. Hon. Rotimi Amaechi ya tabbatar da ficewarsa daga jam'iyyar APC.

Rotimi Amaechi ya ce Najeriya ta lalace gaba ɗaya kuma tana buƙatar sauyi na gaske domin dawo da martabarta.

Ministan Buhari ya watsar da jam'iyyar APC
Rotimi Amaechi ya tabbatar da ficewarsa daga jam'iyyar APC. Hoto: Rt. Hon. Rotimi Amaechi.
Asali: Facebook

Amaechi ya tabbatar da ficewarsa daga APC

Amaechi, wanda ya taba zama gwamnan Jihar Rivers, ya kuma zargi jam’iyyar APC da INEC da haɗin kai wajen magudin zaɓe, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana bayan ƙaddamar da shugabancin rikon kwarya na jam’iyyar ADC a Abuja, ya ce talauci ya yi yawa, mutane ba sa iya cin abinci.

Amaechi ya ce ya fice daga APC daren Talata, ya kuma yi mamakin yadda ba su kore shi daga jam’iyyar ba tun da farko.

Da aka tambaye shi meyasa bai goyi bayan gwamnati ba, sai ya ce:

"A’a, ba wai sauya gwamnati ba, sai dai sauya Najeriya gaba ɗaya, Najeriya ta lalace gaba ɗaya. Mutane ba sa iya cin abinci, babu kuɗi, Komai ya ƙare, tsadar rayuwa ta kai kololuwa.
“Gwamnatin tarayya maimakon gyara zaɓe, sai ta nemi lalata shi. INEC na taimaka musu wajen magudin zaɓen.
“A’a, abin da ya kamata shi ne mu kafa wata tafiya, ba kawai jam’iyya ba, inda 'yan Najeriya za su karɓi iko da kansu.”

Amaechi ya caccaki gwamnatin APC a Najeriya
Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi ya bar APC. Hoto: Rt. Hon. Rotimi Amaechi.
Asali: Twitter

Amaechi ya fadi lokacin da ya bar APC

Da aka tuna masa cewa yana cikin gwamnati kuma ya shafe shekara biyu a APC ƙarƙashin Tinubu, sai ya ce ya fice daren Talata 1 ga watan Yulin 2025, Daily Post ta tabbatar.

“Na bar APC daren jiya, ban halarci wani taro ba, lokacin ƙarshe da suka gayyace ni, na ce kada su sake gayyata.
“Gaskiya ma na yi mamakin yadda ba su kore ni ba, na rubuta musu cewa kada su sake gayyata ta taro.
“Ba za ka kasance a inda mafi yawan mutane ke sata ba, kai kuma ba ka ce komai ba.”

Cewar Amaechi

Abubakar Malami ya yi murabus daga APC

Mun ba ku labarin cewa tsohon ministan shari'a Abubakar Malami ya fice daga jam’iyyar APC inda ya ce Najeriya na cikin mawuyacin hali.

Malami ya ce matsalolin tsaro da na tattalin arziki sun jefa talakawa cikin wahala, yayin da gwamnati ke fifita siyasa fiye da rayukan jama'a.

Ya ce shiga ADC domin kishin kasa da yunkurin ceto Najeriya daga halin da take ciki wanda ya jefa al'umma cikin tulin matsaloli.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.