Mai Mala Buni
Yayin da ya rage kasa da awanni 24 a fara gudanar da zanga Zanga a fadin kasar nan, gwamnatin jihar Yobe ta zauna da shugabannin hukumomin tsaro.
Gamayyar malaman addinin Musulunci a jihar Ogun sun yi Allah wadai da shirin gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya inda suka shawarci matasa kan haka.
Fusatattun matasa a jihar Yobe sun yaga allunan titi ɗauke da hotunan shugaba Tinubu, Kashim Shettima mataimakinsa da kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.
Gwamnatin jiha Yobe ta sanar da kammala shirye shiryen karbar shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ziyarar kaddamar da ayyuka ciki har da raba kayan tallafi.
Gwamnatin Mai Mala Buni ta roki al'umar jihar Yobe da su guji shiga zanga-zangar gama gari da wasu ke kokarin haɗawa a kasar nan saboda matsin tattalin arziki.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana dalilin da ya sanya ake samun karuwar matsalar rashin tsaro a jihar. Gwamnan ya ce laifin ta'ammali da kwayoyi ne.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya kara yawan majalisar zartaswar jihar. Gwamnan ya rantsar da sababbin kwamishinoni guda biyu da wasu hadimai.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya dakatar da shugaban karamar hukumar Machina a jihar. Gwamnan ya yanke hukuncin ne bisa wasu zarge-zarge da ake yi masa.
Rundunar sojojin Najeriya ta yi nasarar dakile harin Boko Haram kan karfunan wutar lantarki domin lalata su a bayan garin Damaturu da ke jihar Yobe.
Mai Mala Buni
Samu kari