'Na Wucin Gadi ne,' El Rufa'i Ya Yi Magana kan Taruwa a ADC don Doke Tinubu a 2027
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i ya bayyana dalilin da ya sa yan adawa suka rungumi ADC a madadin SDP
- A ranar Laraba ne manyan yan adawar kasar nan suka bayyana amfani da jam'iyyar ADC wajen cimma masufarsu a 2027
- El-Rufa'i, ya ce an dauki ADC ne saboda saukin matsalolin cikin gida, amma duk da haka ana dakon INEC kan rajista sabuwar jam'iyya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana cewa ‘yan adawa za su iya fafatawa da jam’iyyar APC a babban zaɓe mai zuwa.
Ya ce hakan na daga cikin dalilan da ya sa suka amince da amfani da jam’iyyar ADC domin cimma manufofinsu na ceto Najeriya.

Asali: Facebook
A wata hira da ya yi da RFI Hausa, El-Rufa’i ya ce har yanzu suna cikin tsarin rajistar sabuwar jam’iyya, duk da cewa an amince da tafiya a turbar ADC.
El-Rufa'i: Dalilin ‘yan adawa na raba kafa
Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa gwamnati mai ci na iya shiga duk wata sabuwar jam’iyya da ‘yan adawa suka koma domin kawo masu cikas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce sun amince da tafiya a cikin ADC ne saboda ita ce mai sauƙin matsaloli idan aka kwatanta da waɗansu jam'iyyun da ake harin tafiyar haɗaka a ciki.
A kalaman El-Rufa'i:.
"Wannan shigar mu ADC na wucin gadi ne. Idan Allah Ya sa aka samu wata jam’iyya marar matsala... Misali, ni ɗan jam’iyyar SDP ne, kuma ban fice daga jam’iyyar ba har yanzu."
"Ina nan ina ƙoƙarin ganin ta zama jam’iyyar haɗaka. Amma wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar SDP sun riga sun koma ma’aikatan gwamnati."
El-Rufa’i ya zargi gwamnati da katsalandan
Tsohon jigo a jam’iyyar APC, Malam Nasir El-Rufa’i, ya yi zargin cewa gwamnatin APC da ke shugabancin Najeriya na jawo wa ‘yan adawa matsaloli.
A cewarsa, gwamnati na ƙoƙarin amfani da wasu a cikin jam’iyyun adawa domin kawo hargitsi, kamar yadda aka gani a SDP.

Asali: Facebook
El-Rufa'i ya ce:
"Wannan ADC da muka shiga ma, kar ka yi mamaki nan da ‘yan kwanaki ko watanni wasu su fito su ce a’a, su ne ‘yan jam’iyyar ADC kuma ba a gaya musu ba — za su garzaya kotu."
Ya kuma yi zargin cewa gwamnati na iya biyan wasu daga cikin ‘yan adawa kuɗi don a yi ta buga shari’a da nufin kawo musu cikas.
Sai dai, tsohon gwamnan ya nuna damuwa cewa babu tabbas ko hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) za ta tabbatar masu da rajistar jam’iyyar da suke ƙoƙarin kafa wa.
Atiku, El-Rufa'i sun kaddamar da jam'iyyar adawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitattun ‘yan adawa sun hallara a cibiyar Yar’Adua da ke Abuja tare da amincewa da ADC a matsayin jam'iyyar hadaka.
Daga cikin manyan ‘yan siyasar da suka halarci taron akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi.
Wasu fitattun mutane da suka halarci taron sun haɗa da tohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung da Mashahurin ɗan jarida kuma jigo a PDP, Dele Momodu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng