Plateau: Yayin da Ake Watsewa Tinubu, Hadimin Gwamna Ya Ajiye Aiki, Ya Dawo APC
- Wani a gwamnatin Plateau ya yi murabus daga mukamin mai ba gwamnan jihar, Caleb Mutfwang shawara kan harkokin siyasa
- Letep Dabang ya ajiye mukaminsa a hukumance ranar 30 ga Yuni, 2025 inda ya tabbatar da komawa jam'iyyar APC
- Dabang ya bayyana godiyarsa ga damar da aka ba shi ya yi aiki da gwamnati, kuma ya ce yana fatan gwamnati za ta ci gaba da samun nasara
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya rasa daya daga cikin hadimansa kan harkokin siyasa.
Mai ba gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang shawara kan harkokin siyasa, Letep Dabang ya ajiye aikinsa.

Source: Facebook
Murabus dinsa yana kunshe ne cikin wata wasika da aka rubuta ranar 30 ga Yuni, 2025, wacce aka aika wa shugaban ma’aikatan gwamnan, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda APC ta yi rashin jiga-jigai a Abuja
Hakan na zuwa ne bayan jam'iyyar APC ta tafka asarar wasu daga cikin jiga-jiganta yayin da ake maganar hadakar jam'iyyun adawa.
Tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami SAN ya fice daga jam’iyyar APC, yana cewa Najeriya na cikin mawuyacin hali a yau.
Haka nan tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi shi ma ya tabbatar da ficewarsa daga jam'iyyar da ya rike muƙamin minista.
Malami ya ce matsalolin tsaro da na tattalin arziki sun jefa talakawa cikin wahala, yayin da gwamnati ke fifita siyasa fiye da rayukan jama'a.

Source: Twitter
Hadimin Gwamna ya koma APC bayan murabus
Dabang ya sanar da wakilan gwamnan jihar murabus din a yau Laraba inda ya yi godiya ta musamman kan damar da aka ba shi.
Daga bisani, bayan godiya ga Gwamna Caleb Mutfwang, ya yi masa fatan alheri da samun nasara, cewar rahoton Tribune.
Sanarwar ta ce:
“Don Allah a karɓi wannan wasika a matsayin sanarwa ta hukuma kan murabus dina daga matsayin mai ba da shawara kan harkokin siyasa.
“Na yaba da damar da aka ba ni na yin hidima da bayar da gudunmawa ga gwamnati a matsayin mai ba da shawara.
"Na kuma kasance tsohon Darakta Janar na yakin neman zaben shugaban kasa/gwamna na PDP a Jihar Filato.
“Na gode da damar da aka bani, kuma ina fatan gwamnatin za ta ci gaba da samun nasara."
An kuma gano cewa Dabang, wanda tsohon shugaban APC ne a jihar, ya koma jam’iyyar da ta yi shekaru takwas tana mulki kafin 2023.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar a yanzu, Rufus Bature, ya tabbatar da cewa:
“Eh, yana tare da mu, ya dawo cikakke, a siyasa, babu abokin gaba na dindindin, sai dai neman muradi su tafi tare.”
An zabi kakakin majalisar jihar Plateau
Mun ba ku labarin cewa kakakin majalisar Plateau, Hon. Gabriel Dewan, ya yi murabus, inda aka zaɓi Nanloong Daniel na APC a matsayin sabon shugaba.
Hakan ya biyo bayan taron sirri da Gwamna Caleb Mutfwang don warware rikicin shugabanci da rashin daidaiton siyasar jihar.
Majiyoyi sun ce an sa ran jagorancin Hon. Daniel zai dawo da zaman lafiya da ci gaba ga majalisar Plateau, tare da haɗin gwiwa tsakanin bangarorin gwamnati.
Asali: Legit.ng


