Kwankwaso Ya Rasa Tikitin Takarar Shugaban Kasa na NNPP a 2027, An Faɗi Dalili
- Rikicin jam'iyyar NNPP na ƙara tsananta tun bayan fara yaɗa jita-jitar cewa Kwankwaso na shirin sauya sheƙa zuwa APC
- Tsagin Dr. Major Agbo ya bayyana cewa NNPP ba za ta sake bai wa Kwankwaso tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027 ba
- Agbo ya yi wannan magana ne a matsayin martani ga Buba Galadima, wanda ya ce Kwankwaso zai sake tsayawa takara a inuwar NNPP
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsagin NNPP ya bayyana cewa jam'iyyar ba za ta sake ba Rabiu Musa Kwankwaso tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba.
Shugaban tsagin NNPP, Major Agbo, ya ce Kwankwaso wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar a zaɓen 2023, ba zai samu dama ta biyu ba.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta tattaro cewa Agbo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar yau Asabar, 5 ga watan Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsagin NNPP ya maida martani ga Buba Galadima
Dr. Major Agbo ya mayar da martani ne ga maganganun Buba Galadima wanda ya ce Kwankwaso zai ci gaba da zama a NNPP kuma zai sake yin takarar shugaban ƙasa a 2027.
Galadima ya ce babu wata shaida da ke nuna cewa Kwankwaso na shirin komawa jam’iyyar APC kamar yadda ake ta hasashe.
Ya ce Kwankwaso da magoya bayansa za su “ci gaba da kasancewa a NNPP har sai lokacin da aka buga gangar fara siyasar 2027."
Galadima ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su mara masa baya domin ya karɓi shugabancin ƙasar nan domin dawo da komai kan turba.
NNPP ta nanata korar Kwankwaso & Buba
Da yake martani, Dr. Agbo Major ya ce tuni NNPP ta kori Kwankwaso da Galadima saboda laifin cin amanar jam’iyya, kuma ba za su sake amfani da jam'iyyar ba.
“Jam’iyyar NNPP ta kori Kwankwaso da Galadima tun tuni, don haka ba su da hurumin magana a madadinmu kuma ba za su sake amfani da dandalin jam’iyyar ba.”
“Ƙawancen da muka ƙulla da Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Kwankwaso ya ƙare ne jim kaɗan bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
"Ba za mu sake yarda da Kwankwaso ba, ko da menene, saboda matsalolin da ya jefa mu ciki da rigingimun cikin gida. Ya kai mu gaban kotu ba gaira ba dalili, ya kuma sauya tambarin jam’iyya."
- Agbo Major.

Asali: Twitter
NNPP za ta tsaida Kwankwaso takara a 2027?
Ya ce sai da kotuna suka shigo ciki suka tilasta wa INEC ta dawo da asalin tambarin NNPP bayan wani taron jam’iyya da Kwankwaso ya kira “na bogi” a Abuja.
“Kwankwaso yana tunanin za a sake ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa kamar yadda aka yi a 2023, amma hakan ba zai faru ba,” in ji shi.
A ƙarshe, Dr. Agbo Major ya shawarci ‘yan Najeriya da su yi watsi da kalaman Kwankwaso da magoya bayansa waɗanda ke nuna har yanzu suna nan daram a NNPP.
Da gaske Kwankwaso na shirin komawa APC?
A baya, kun ji cewa shugaban jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano, Hashimu Dungurawa ya ce jagoransu, Rabiu Kwankwaso ba ya shirin sauya sheƙa zuwa APC.
Ya ce duk da labarin da ake yaɗawa ba gasƙiya ba ne, amma ya kara fito da amana da nagartar jagoran ɗarikar Kwankwasiyya.
Dugunrawa ya kuma bayyana cewa akwai tsohuwar alaka ta siyasa tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kwankwaso.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng