Kwankwaso Zai Koma APC bayan Ganduje Ya Yi Murabus? Shugaban NNPP na Kano Ya Yi Bayani

Kwankwaso Zai Koma APC bayan Ganduje Ya Yi Murabus? Shugaban NNPP na Kano Ya Yi Bayani

  • Shugaban NNPP reshen jihar Kano, Hashimu Dungurawa ya ce jagoransu, Rabiu Kwankwaso ba ya shirin sauya sheƙa zuwa APC
  • Dungurawa ya ce labarin da ake ta yaɗawa jita-juta ce kawai amma babu wani shiri da Kwankwaso ke yi na haɗewa da Shugaba Tinubu
  • Ya ce Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da Kwankwaso abokai ne da suka san juna lokacin suna gwamnonin jihohin Kano da Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Shugaban jam’iyyar NNPP a jihar Kano, Hashimu Dugunrawa, ya musanta jita-jitar cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai sauya sheƙa zuwa APC.

Dungurawa ya bayyana cewa babu wani shiri da Kwankwaso, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP ke yi na haɗewa da APC, ya ce jita-jita ce kurum.

Sanata Kwankwaso ba zai koma APC ba.
Shugaban NNPP na Kano ya ce rahoton Kwankwaso na shirin komawa APC jita-jita ce kawai Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Shugaban NNPP ta Kano ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Tribune Nigeria ta wayar tarho ranar Talata, 1 ga watan Yuli, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da gaske Kwankwaso na shirin komawa APC?

Sai dai, a cewar Hashimu Dungurawa, duk da cewa labarin jita-jita ce kawai, “muna farin ciki cewa mutane na yaɗa ta.”

"Sanata Kwankwaso, jagoranmu, mutum ne da ake ganinsa da mutunci kuma mai muhimmanci a fagen siyasa.”
“Mutane na da tabbaci cewa Sanata Kwankwaso ba barawo ba ne, ba ɗan damfara ba ne, kuma ba ɗan siyasa marar amfani ba ne.
"Mutum ne da Allah Ya azurta da gaskiya da rikon amana, kuma ɗan siyasa ne mai hangen nesa.”

- Hashimu Dungurawa.

NNPP na farin ciki da yaɗa jita-jitar Kwankwaso

Dugunrawa ya kuma bayyana cewa akwai tsohuwar alaka ta siyasa tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kwankwaso.

A rahoton Daily Post, ya ƙara da cewa:

“Batun da ake yaɗawa cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP na shirin sauya sheƙa jita-jita ce kawai.
“Sai dai muna godiya ga Allah cewa ana yaɗa wannan jita-jita ta hanyar da za ta amfane mu, saboda tana bayyana wa duniya irin farin jinin da Kwankwaso ke da shi. “Ni dai, ba zan iya gina wani abu a kan jita-jita ba.”

Jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso.
Rabiu Kwankwaso na nan daram a jam'iyyar NNPP Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Kwankwaso da Tinubu abokan juna ne

Shugaban NNPP na Kano, Dugunrawa ya kuma nanata cewa Kwankwaso abokin Shugaba Tinubu ne tun da daɗewa, musamman lokacin da suke gwamnoni daga 1999 zuwa 2003.

“Shugaba Tinubu tsohon gwamnan jihar Lagos ne, Sanata Kwankwaso kuma tsohon gwamnan jihar Kano ne. Dukkansu sun taɓa zama sanatoci, ma’ana sun wakilci jihohinsu a majalisar dattawa.
“Don haka ba baƙin juna ba ne, sun jima da sanin juna. Amma a halin yanzu, batun sauya sheƙar Sanata Kwankwaso zuwa APC jita-jita ce kawai," in ji shi.

Ƴan Kwankwasiyya sun caccaki Ganduje

A wani rahoton, kun ji cewa ƴan Kwankwasiyya sun bayyana cewa tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya jawo wa Kano abin kunya.

Wannan na zuwa ne bayan murabus da tsohon gwamnan Kano, Ganduje ya yi daga kujerar shugaban jam’iyyar APC.

Wasu daga cikin 'yan Kwankwasiyya, sun bayyana cewa Ganduje ya batawa al’ummar Kano suna, kuma hakan ne ya sa aka tilasta masa yin murabus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262