Buba Galadima Ya Tabbatar da cewa APC na Son Jawo Kwankwaso daga NNPP

Buba Galadima Ya Tabbatar da cewa APC na Son Jawo Kwankwaso daga NNPP

  • Buba Galadima ya ce Rabiu Kwankwaso shi ne ɗan siyasar da Najeriya ke buƙata kuma ya dace a mara masa baya
  • Tsohon ɗan siyasa kuma jigo a NNPP ya bayyana Kwankwaso a matsayin jagora mai nagarta da gogewa a harkar mulki
  • Ya musanta jita-jitar cewa Kwankwaso zai koma jam’iyyar APC, yana mai cewa har yanzu yana nan daram a NNPP

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babban jigon jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin ɗan siyasar da Najeriya ke buƙata.

Ya bayyana haka ne yana mai cewa babu wani ɗan siyasa da ya kai shi daraja da kwarewa a yanzu a kasar nan.

Buba Galadima ya ce Kwankwaso ne ya kamata ya shugabanci Najeriya
Buba Galadima ya ce Kwankwaso ne ya kamata ya shugabanci Najeriya. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Asali: Facebook

Buba Galadima ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Arise TV, inda ya ce Kwankwaso yana da kima, nagarta da cancanta da zai iya sauya tafiyar da Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Kwankwaso na da ƙwarewa,' Buba Galadima

Buba Galadima ya ce shaharar da Kwankwaso ke samu a cikin mutane ba wai daga kuɗi ko ɗaukaka ne ta hanyar kamfen ba, illa dai nagartarsa ce da kwarewar sa da mutane ke yabawa.

Ya ce:

“A yau, mutane ne suke yi wa Kwankwaso kamfen kyauta. Ba don kuɗi ba, ba don matsin lamba ba. Wannan yana nuni da cewa jama’a sun fahimci cewa shi ne ya dace da Najeriya.”

Ya ƙara da cewa Kwankwaso yana da nagarta, tsari da hangen nesa wanda idan aka ba shi dama zai iya sauya salon mulkin da ya daɗe yana tangal-tangal.

Buba: 'APC, PDP na neman Kwankwaso'

Galadima ya bayyana cewa labaran da ke yawo cewa Kwankwaso zai koma jam’iyyar APC ba su da tushe, yana mai cewa Kwankwaso yana nan daram a NNPP.

Ya ce:

“Mun ji ana cewa Ganduje ya sauka ne don a bai wa Kwankwaso hanya. Amma babu wata hujja da ke nuna cewa Kwankwaso yana shirin komawa APC.

"Har ma wasu sun ɗora hotonsa da katin zama dan APC, amma duk ƙarya ne.”

A cewarsa, ko da jam’iyyun PDP, APC da sabuwar tafiyar ADC suna kokarin jawo Kwankwaso, amma shi yana da tsari kuma ba zai yi gaggawar barin NNPP ba sai lokacin ya yi.

Buba Galadima a wajen wani taron NNPP.
Buba Galadima a wajen wani taron NNPP. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Asali: Facebook

A cewarsa, Kwankwaso ya cancanci zama shugaban kasa saboda irin nagartar da ya nuna a rayuwarsa ta siyasa da kuma irin karɓuwa da yake da ita musamman a Arewacin Najeriya.

Ya jaddada cewa Kwankwaso ne mutumin da zai iya ceto Najeriya daga matsalolin da take ciki, yana mai kira ga ’yan Najeriya da su hada kai domin mara masa baya a gaba.

APC ta zargi NNPP na jawo mata rikici

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC a jihar Kano ta zargi NNPP mai mulki a jihar da kunna mata wutar rikici.

Hakan na zuwa ne bayan wata kungiya mai suna 'APC kadangaren bakin tulu' ta bukaci shugaban jam'iyya na jihar ya sauka.

Kungiyar ta ce shugaban jam'iyyar, Abdullahi Abbas na neman wa'adi na uku bayan kammala lokacin da doka ta tanadar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng