"Abu 1 Zai Haɗa Faɗa," Jerin Manyan Jiga Jigai 3 da Ka Iya Tarwatsa Jam'iyyar Haɗaka, ADC
A ranar Laraba da ta gabata, kungiyar haɗakar ƴan adawar Najeriya ta zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar da za ta ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Tun bayan wannan lokaci labarin wannan haɗaka ya mamaye kafafen sada zumunta, duk da dai hakan bai zo wa ƴan Najeriya da mamaki ba.

Asali: Facebook
Dalilin kafa haɗakar ADC kafin 2027
Premium Times ta tataro cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ne ke jagorantar wannan haɗaka tare da Peter Obi da Nasir El-Rufai da jiga-jigan siyasa da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wajen ƙaddamar da haɗakar, shugaban ADC na riko, David Mark, ya ce wannan yunƙuri ne na ceton dimokuraɗiyyar Najeriya da hana ƙasar ta koma jam’iyya ɗaya ke mulki.
Burin jagororin adawa 3 na iya tarwatsa ADC
Sai dai masana sun ce akwai abu ɗaya da ka iya ruguza wannan haɗaka, wanda shi ne tikitin takarar shugaban ƙasa.
Ana ganin son zuciya da ra'ayin wasu daga cikin jagororin adawa kan yankin da ya kamata ya fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, ka iya zama cikas a shirin haɗakar ADC.
1. Atiku na da burin sake neman takara
Duk da har yanzu akwai lokaci kafin a fitar da ‘yan takara a hukumance, masu sharhi na siyasa na hasashen cewa Atiku Abubakar, mai shekara 78 zai sake tsayawa takara.
Masoyansa na ganin cewa kasancewarsa tsohon mataimakin shugaban ƙasa shi kaɗai a cikin masu neman kujerar, hakan ya sa ya fi cancanta fiye da kowa.
Sai dai har yanzu, Atiku, wanda ya jima yana takarar shugaban ƙasa a jam'iyyu daban-daban, bai fito ya bayyana aniyarsa ba a wannan karo.
2. Amaechi ya yi alƙawarin yin wa'adi ɗaya
Baya ga Atiku, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa karkashin jam'iyyar haɗaka ADC a shekarar 2027.
A wata tattaunawa da aka yi da shi a Channels TV a ranar Alhamis, Amaechi ya ce yana ganin ya kamata a mutunta yarjejeniyar rabon mulki tsakanin Arewa da Kudu.
Ya tuna yadda ya jagoranci yaki da gwamnatin PDP a 2015 saboda gwamnati ta ƙi bin yarjejeniyar cewa za ta yi mulki na tsawon shekaru huɗu kacal.
Tsohon ministan ya ce:
“Na jagoranci yaki da gwamnatin PDP. Me ya sa? Saboda an yi yarjejeniya cewa za a yi shekara huɗu kacal. Amma daga baya gwamnati ta karya alkawarin, na ce hakan bai dace ba.”
Amaechi ya ƙara da cewa, bisa ga tsarin rabon mulki, idan har ya samu damar shugabancin ƙasa a 2027, zai yi shekaru huɗu ne kacal ya sauka ya ba ɗan Arewa.
3. Peter Obi ya bi sahun Amaechi
Ra’ayin Amaechi ya yi daidai da na tsohon gwamnan Anambra, Mr. Peter Obi, wanda ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Obi ya bawa mutane mamaki lokacin da ya lashe jihohi 11 daga cikin jihohi 36 da Abuja. Obi ma ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a 2027 a karkashin haɗakar ADC.
A saboda haka, Obi da Amaechi na fatan ADC za ta ba Kudu tikitin takarar shugaban ƙasa, kuma idan ɗan kudun ya yi nasara, zai yi wa’adi ɗaya kacal kafin mulki ya koma Arewa.

Asali: Twitter
Babban kalubalen da ke gaban ADC
Amma Atiku, wanda tun shekarar 1993 ya ke ƙoƙarin zama shugaban ƙasa, ana sa ran zai ƙalubalanci wannan ra’ayi kuma ya nemi zama ɗan takarar ADC.
Yayin da ƙawancen ke shirin karbe mulki a 2027, babban ƙalubalensu shi ne yadda za su tsaida wanda ya fi cancanta kuma daga wane yanki ya kamata ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito.
PDP ta rasa babban jigonta a Gombe
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Shugaban Kwamitin Sulhu na Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe, Air Vice Marshal (AVM) Shehu Adamu Fura ya koma ADC.
AVM Shehu ya sanar da ficewarsa daga babbar jam'iyyar adawa watau PDP tare da komawa jam'iyyar haɗaka domin kifar da gwamnatin APC.
Tsohon sojan Saman Najeriya ya bayyana cewa matakin da ya dauka ya biyo bayan tattaunawa da nazari mai zurfi da ya yi.
Asali: Legit.ng