Dubu Ta Cika: An Kama Wani Mai Taimaka Wa Yan Ta'adda a Filin Jirgin Sama a Jihar Yobe
- Dakarun sojoji sun yi nasarar damke wani mutumi da ake zargin dan leken asirin kungiyar Boko Haram ne a filin jirgin sama na jihar Yobe
- Rahoto ya nuna cewa bayan kama mutumin, sojoji sun mika shi sashen leken asiri na rundunar Operation Hadin Kai domin ci gaba da bincike
- Wannan dai na zuwa ne yayin da hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP ke karuwa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Yobe, Nigeria - Jami'an rundunar sojin Najeriya sun cafke wani da ake zargin yana taimaka wa yan ta'adda da bayanan sirri a filin jirgin sama a jihar Yobe.
Dakarun rundunar Operation Hadin Kai ne suka samu wannan nasara, inda suka kama wanda ake zargi da ba ‘yan Boko Haram da ISWAP bayanai a filin jirgin sama na Muhammadu Buhari International Cargo Airport da ke jihar Yobe.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani

Source: Facebook
Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ya tabbatar da hakan a shafinsa na X jiya Juma'a, 24 ga watan Afrilu, 2026.
Yadda aka kama wanda ake zargi
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kama mutumin ne da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilu, 2026.
Dakarun sashe na 2 na rundunar sojin Operation Hadin Kai da ke aiki a filin jirgin ne suka kama shi bayan sun lura da yadda yake zirga-zirga cikin shakku a kusa da sansanin soji.
Matakin da aka dauka bayan kama shi
Majiyoyin sun ce wanda ake zargin bai bayar da wani bayani mai amfani ba lokacin da aka fara yi masa tambayoyi tun a filin jirgin saman, lamarin da ya sa aka fara zarginsa.
Daga bisani dakarun sojojin sun miƙa shi ga sashen leƙen asirin soji domin ci gaba da gudanar bincike, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Source: Twitter
An kuma bayyana cewa duk da cewa ana ganin zaman lafiyaya dawo a yankin a halin yanzu, amma har yanzu akwai rashin tabbas kan abin da ka iya zuwa ya dawo.
Wani dan jihar Sakkwato da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Legit Hausa cewa akwai bukatar gwamnati ta tashi tsaye domin tabbatar da tsaro a kauyukan jihar.
Ya ce matsalar ta wuce duk inda mutane ke tsammani, domin mutane na rasa muhallansu saboda gudun hare-haren 'yan bindiga.
"Jami'an tsaro suna kokari daidai gwargwado amma har yanzu matsalar ta fi karfinsu a wurare da dama, za ka ga jami'ai 10 ko 20, taya za su tunkari 'yan bindiga sama da 200.
"Muna kira ga gwamnati ta kara dagewa wajen ganin an samar da tsaro kafin zuwa damina," In ji shi.
Sojoji sun kashe mayakan ISWAP 20
A wani labarin, kun ji cewa dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun kashe aƙalla mambobi 20 na ƙungiyar Boko Haram/ISWAP, a jihar Yobe.

Kara karanta wannan
Al'umma sun samu saukin hare hare, hatsabibin dan ta'addan ISWAP ya bakunci lahira
Daga cikin 'yan ta'addan da aka kashe har da wani kwamanda da aka bayyana matsayin Abu Yusu, Munzir na Dursula a Goniri da ke ƙaramar hukumar Gujba a jihar Yobe.
An samu wannan nasara ne yayin da ’yan ta’addan sun yi yunkurin kai hari kan sansanonin sojoji ne da ke ƙarƙashin Sassa na 2 na Operation Hadin Kai (OPHK).
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
