Tarin 'Yan ADC Sun Yi Gangamin Farko domin Tarbar Sakataren Jam'iyyar a Legas

Tarin 'Yan ADC Sun Yi Gangamin Farko domin Tarbar Sakataren Jam'iyyar a Legas

  • Masu goyon bayan Rauf Aregbesola sun taru a filin jirgin Legas don tarbar sa daga Abuja bayan nada shi sakataren ADC
  • Tsohon ministan cikin gida ya ce babu bukatar zagi ko fada da kowa, sai dai tattaunawa kan matsalolin Najeriya
  • Rauf Aregbesola ya bukaci magoya bayan jam'iyyar su nuna gaskiya da dalilai masu kyau don kare matsayar ADC a siyasance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Magoya bayan tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, sun mamaye filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Juma’a domin tarbar sa daga Abuja.

Aregbesola da aka nada sabon sakataren riko na jam’iyyar ADC, ya samu tarba ta musamman daga mabiyansa da suka nuna karfin gwiwa da karsashi a sabuwar tafiyar da suka fara.

'Yan ADC yayin tarbar sakataren jam'iyyar a Legas.
'Yan ADC yayin tarbar sakataren jam'iyyar a Legas. Hoto: Rauf Aregbesola
Asali: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa Rauf Aregbesola ya yi jawabi ga magoya bayan shi yayin taron kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu tarbar sa sanye da huluna ruwan dorawa, sun rera taken siyasa da daga alluna domin murnar matakin da Aregbesola ya dauka na komawa sahun jagororin jam’iyyun adawa.

ADC na son kara karfi kafin zaben 2027

Rahotanni daga jaridar Tribune sun bayyana cewa Aregbesola na cikin sahun jagororin da suka karɓi mukamai a ADC.

ADC ce a yanzu ta zama cibiyar sabuwar kawancen da ke shirin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027.

Jam’iyyar na samun goyon bayan fitattun ‘yan siyasa irinsu tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na LP a 2023, Peter Obi da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.

Masu sharhi na ganin cewa wannan haɗin gwiwa da ADC ke jagoranta na iya canza akalar siyasar Najeriya idan aka ci gaba da tafiyar da ita da kwanciyar hankali da manufa mai ma’ana.

Aregbesola ya bayyana manufar jam'iyyar ADC

Bayan sauka daga jirgi, Aregbesola ya yi jawabi ga magoya bayansa inda ya nuna godiya da kuma sharhi kan abinda ke gaban su a matsayin sabuwar jam’iyya.

Ya ce:

“Na gode wa dukkan ‘ya’yan ADC da suka fito domin tarbar mu. Aikin da ke gabanmu yana da girma. Amma ba lallai sai mun yi zagi ko fada da kowa ba,”

Ya ce maimakon zagi, ‘yan ADC su dinga tambayar mutane:

“Shin rayuwar ‘yan Najeriya ta fi ta da, ko ta lalace?”

Ya kara da cewa kamata ya yi a tattauna da hujjoji kan hauhawar farashin kaya, koma bayan tattalin arziki, da tsananin talauci.

Aregbesola da wasu 'yan ADC yayin taro a Abuja.
Aregbesola da wasu 'yan ADC yayin taro a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Aregbesola ya ja kunnen mabiyansa da su kauce wa cin mutunci, su dage da bayani da hujjoji wajen kare matsayin ADC a siyasa.

Jam'iyyar ADC na fatan samun gwamnoni 5

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta ce tana fatan samun karin gwamnoni biyar nan kusa kadan.

Wani jigon jam'iyyar a jihar Katsina ya bayyana cewa gwamnonin sun riga sun ba su tabbacin cewa za su sauya sheka.

Tsohon shugaban jam'iyyar ya ce ba za su bayyana sunan gwamnonin da suke magana da su ba a yanzu saboda wasu dalilai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng