An Raba Hanya: LP Ta Bukaci Peter Obi Ya Je Ya Hade da Masu Hadaka a Jam'iyyar ADC
- Bangaren Julius Abure na LP ya umurci Peter Obi da ya fice daga jam’iyyar cikin sa’o’i 48 bayan shiga kawancen jam’iyyu
- Jam’iyyar ta ce ba za ta lamunci ‘yan siyasa masu tafiya da manufofi biyu da ke neman mulki domin kansu ba
- LP ta bayyana cewa sabuwar Najeriya ba za ta samu da hadin gwiwar tsofaffin ‘yan siyasa marasa kishi da son kai ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Bangaren LP da Julius Abure ke jagoranta ya bai wa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, wa’adin sa’o’i 48 da ya fice daga jam’iyyar bayan shiga kawancen 'yan adawa.
Tsagin jam’iyyar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Obiora Ifoh, ya fitar a Abuja.

Asali: Twitter
Punch ta wallafa cewa tsagin jam'iyyar ya ce LP ba za ta taɓa shiga kawancen ADC ba kuma tana kallon mambobin kawancen a matsayin masu neman mulki da son kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
LP ta ce ba za ta shiga kawance a ADC ba
A cewar LP, Peter Obi ya shiga kawancen da ya ƙunshi tsofaffin ‘yan siyasa da suka taɓa mulki kuma suka gaza, kuma hakan ba zai iya haifar da sabuwar Najeriya ba.
Obiora Ifoh ya ce jam’iyyar na da masaniya cewa Peter Obi yana ta ganawa da wasu daga cikin mambobin jam’iyyar da nufin janyo su su shiga sabuwar jam’iyyarsa.
Sai dai Obiora Ifoh ya ce suna da labarin cewa da dama daga cikin su sun ƙi amincewa da wannan matakin.
Ya ce:
“Dukkan ‘ya’yan jam’iyyar da suka shiga wannan kawance, muna ba su wa’adin sa’o’i 48 su fice daga jam’iyyar mu, domin LP ba wurin ‘yan siyasa masu raba kafa ba ne.”
Dalilin LP na kin shiga hadaka a ADC
A cewar Ifoh, galibin mambobin kawancen ‘yan siyasa ne da suka daɗe suna mulki ba tare da kawo ci gaba ba.
Ya ce jam’iyyar LP ce kadai ke da cancanta ta jagoranci matasa da sauran ‘yan Najeriya zuwa sabuwar ƙasar da ake fatan samarwa.
Obi ya ce kawance ne kaɗai zai kawo canji
A halin da ake ciki kuma, Peter Obi ya goyi bayan kawancen jam’iyyun adawa da ke neman karɓe mulki daga hannun shugaban ƙasa Bola Tinubu a 2027.
A sakon da ya wallafa a X, Obi ya ce babu wata jam'iyya guda da za ta iya sauya Najeriya ita kaɗai, don haka akwai buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe domin cimma burin canjin ƙasa.

Asali: Twitter
Obi ya ce yana maraba da duk wani yunkuri da zai haifar da cigaba da haɗin kan jam’iyyun adawa domin samar da shugabanci na gaskiya da rikon amana.
Fadar shugaban kasa ta caccaki hadakar ADC
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi tir da matakin da 'yan adawa suka dauka na yin hadaka a ADC.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce kiyayya ga Bola Tinubu ne ta sanya mutanen yin hadaka.
Bayo Onanuga ya ce yawancin wadanda suka shiga hadakar daga APC sun riga sun fita tun da dadewa daga jam'iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng