'Babu Abin da zai Raba ni da Buhari': Tsohon Minista Ya Musanta Barin Jam'iyyar APC
- Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya karyata rahotannin cewa ya fice daga jam’iyyar APC zuwa sabuwar kawancen adawa
- Sirika ya bayyana a kafar sadarwa cewa har yanzu yana tare da Buhari da jam’iyyar APC, yana mai kiran labaran karya da marasa tushe
- Ya soki Wike da Onanuga bisa danganta shi da kawancen, yana mai cewa ya ba APC suna, kuma ba zai fice daga jam’iyyar ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya yi magana kan ikirarin barin jam'iyyar APC.
Hadi Sirika ya karyata rahotannin da ke cewa ya bar jam’iyyar APC zuwa sabuwar kawancen adawa.

Asali: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis 3 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jiga-jigan APC sun watsar da ita
Wannan ya biyo bayan ficewar wasu jiga-jigan APC sun yi watsi da jam'iyyar zuwa ADC domin kwace mulkin Bola Tinubu a zaben 2027.
Daga cikin wadanda suka koma jam'iyyar akwai tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi wanda ya rike minista a mulkin Muhammadu Buhari.
Jiga-jigan yan adawa sun taru a Abuja a ranar Laraba domin ƙaddamar da jam'iyyar ADC saboda kara karfi kafin zaben 2027.
Martanin Hadi Sirika kan rade-radin barin APC
Hadi Sirika ya bayyana biyayyarsa ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC.
Ya kuma soki Ministan Abuja, Nyesom Wike da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga, bisa alakanta shi da kawancen, yana kiran hakan da maras tushe.
“Ina kallon mai girma Nyesom Wike yau a Arise yana cewa na shiga wannan abin da ake kira kawance.
“Yayin da har yanzu ina cikin mamaki, na karanta a Premium Times wani rahoto da aka danganta shi da Chief Bayo Onanuga.

Asali: Twitter
Sirika ya fadi gudunmawarsa a APC
Sirika ya bugi kirji game da gudunmawar da ya ba jam'iyyar APC tun lokacin da aka kafa ta a 2014 domin kwace mulkin PDP.
Tsohon ministan ya ce idan har dole sai mutane sun tsani Muhammadu Buhari to sai dai shi ma a tsane shi saboda yana tare da dattijon a kullum.
Ya kara da cewa:
“Ni ne daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC; ni na ba ta sunanta. Ba ni da niyyar barinta. Zan kasance tare da Buhari.
“Idan lallai dole sai kun tsani Buhari, to ku tsaneni ni ma. Ban da wani uzuri.
“A matakin da suke, ya kamata su duba gaskiyar magana. Ina kira ga mambobinmu na kwarai da su yi watsi da wadannan kalamai marasa inganci."
Ministan Buhari, Abubakar Malami ya bar APC
Kun ji cewa tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami SAN ya fice daga jam’iyyar APC, yana cewa Najeriya na cikin mawuyacin hali a yau.
Malami ya ce matsalolin tsaro da na tattalin arziki sun jefa talakawa cikin wahala, yayin da gwamnati ke fifita siyasa fiye da rayukan jama'a.
Babban lauyan ya ce shigarsa ADC ba cikin fushi ba ne, sai dai kishin kasa da yunkurin ceto Najeriya daga halin da take ciki.
Asali: Legit.ng