Bayan Murabus Ɗin Ganduje, Tsohon Gwamna Ya Ce Umarnin Tinubu Yake Jira

Bayan Murabus Ɗin Ganduje, Tsohon Gwamna Ya Ce Umarnin Tinubu Yake Jira

  • Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Umar Al-Makura, ya yi magana kan shugabancin jam'iyyar APC mai mulki
  • Al-Makura ya bayyana cewa zai karɓi kowane irin matsayi idan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci haka
  • Tsohon gwamnan ya ce idan Tinubu ya umurce shi ya riƙa share tebur a ofishinsa duk Litinin, zai yi hakan da biyayya da ƙwazo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, ya yi martani kan shugabancin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Al-Makura ya bayyana shirinsa na yin aiki a kowane irin mukami idan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kira shi ba tare da bata lokaci ba.

Al-Makura ya yi magana kan muƙamin shugabancin APC
Tsohon gwamna, Tanko Al-Makura ya ce umarnin Tinubu yake jira. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

A wata hira da Trust TV, Al-Makura ya ce shi ɗan jam’iyya ne na gaskiya kuma a shirye yake ya yi duk abin da shugaban ƙasa ya buƙata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jita-jitar alaƙanta Al-Makura da shugabancin APC

Duka wannan na zuwa ne bayan Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga kujerar shugaban jam’iyyar APC.

Wasu jiga-jigai daga tsohuwar CPC da Arewa ta Tsakiya suna so Al-Makura ya gaje shi da sauran yan siyasar yankin.

An musanta murabus din Akume saboda shugabanci

Daga cikin wadanda aka fi kira bayan Al-Makura akwai sakataren gwamnatin tarayya kuma tsohon gwamnan Benue, Sanata George Akume.

An yi ta yada jita-jitar cewa Akume ya ajiye aikinsa domin karbar kujerar Ganduje wanda ya shafe shekaru biyu yana jagorancinta.

Sai dai fadar shugaban kasa ta yi gaggawar fitar da sanarwa inda take musanta labarin da ake yadawa da cewa ba shi da tushe bare makama.

An musanta cewa Akume ya yi murabus daga mukaminsa
Fadar shugaban kasa ta musanta murabus din Akume saboda kujerar Ganduje. Hoto: Sen. George Akume, All Progressives Congress.
Asali: Facebook

Tanko Al-Makura ya fadi burinsa ga Tinubu

A bangarensa, Tanko Al-Makura ya ce shi ba shi da wani zabi da ya wuce ya yi duk abin da zai farantawa Tinubu ransa.

Tsohon gwamnan ya ce duk abin da shugaban kasa yake so ya yi masa shi ne abin da zai yi babu kakkautawa.

Ya ce:

“Ina tabbatar muku cewa idan shugaban ƙasa ya ce ‘Al-Makura, ina so ka riƙa zuwa ofishina ka share min tebur duk Litinin’, zan yarda.
“Wannan ne abin da zai faranta masa rai, kuma yana ganin hakan zai kawo ci gaba ga jam’iyya da ƙasar nan.
“Ina tabbatar muku cewa zan riƙa zuwa duk Litinin a lokaci da aka tsara, in share tebur, in koma gida cikin farin ciki, wannan shi ne matakin da biyayyata da amincina ga shugaba ya kai."

Tinubu ya nada tsohon gwamnan Nasarawa mukami

Mun ba ku labarin cewa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon gwamnan Nasarawa a mukami a hukumar UBEC.

Ministan ilimi Tunji Alausa ne ya jagoranci rantsar da shi yayin wani taro da ya shafi cigaban fasaha a jami’o’i a Abuja.

Tanko Al-Makura zai jagoranci tsara manufofi da dabarun da za su bunkasa ilimi, tare da hadin gwiwa da gwamnoni da kananan hukumomi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.