Masana Taurari Sun Bayyana Abin da zai Faru a Ka’aba ranar Arfa

Masana Taurari Sun Bayyana Abin da zai Faru a Ka’aba ranar Arfa

  • Wani abin mamaki na ilimin taurari zai faru a ranar Arfa ta shekarar 2026, inda rana za ta yi daidai a saman Ka’aba a birnin Makka
  • Masana sun ce wannan lamari yana faruwa ne sau ɗaya cikin shekara 139 idan ya zo daidai da ranar Arfa, kuma ana sa ran zai faru a bana
  • Hukumomin hasashen yanayi na Saudiyya sun ce lamarin ba yana nufin za a samu matsananciyar zafi ba, tare da yin karin bayani game da halin da za a shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Saudi Arabia - Wani abin ban mamaki a fannin ilimin taurari zai faru a bana yayin da rana za ta tsaya kai-tsaye a saman Ka’aba da ke birnin Makka a ranar Arfa, daya daga cikin ranakun da suka fi tsarki a Musulunci.

Kara karanta wannan

An kashe mutum 8 bayan dan majalisa ya bada kyautar miliyoyin Naira a jihar Neja

Masana ilimin taurari sun bayyana cewa lamarin zai faru ne da tsakar rana ranar 27 ga watan Mayun 2026, wanda ya yi daidai da ranar 9 ga watan Zul Hijja 1447 bayan hijira.

Ana sa ran rana za ta kwalle a tsakiyar Ka'aba
Musulman duniya kewaye da dakin ka'aba a Saudiyya Hoto: Haramain
Source: Getty Images

Gulf News ta wallafa cewa A daidai lokacin, rana za ta kasance kai-tsaye a saman Ka’aba, lamarin da zai sa inuwa ta bace gaba daya a birnin Makka na wani dan lokaci.

Ana sa rai da daidaituwar rana a Ka'aba

Jaridar Aminiyar ta ruwaito cewa masana sun ce rana kan yi daidai a saman Ka’aba sau biyu a kowace shekara saboda matsayin birnin Makka da yake kusa da latitude 21.4 a Arewa.

Sai dai abin da ya sa lamarin na bana ya zama na musamman shi ne yadda ya zo daidai da ranar Arfa, abin da aka ce bai taba faruwa ba tun shekarar 1993.

Masana taurari sun ce bambancin da ke tsakanin kalandar Musulunci ta Hijira da kuma kalandar Miladiyya ne ke haddasa wannan daidaituwa, domin kalandar Hijira tana amfani da zagayowar wata wanda ke daukar kusan shekara 139 kafin ya sake komawa kan irin wadannan ranaku na Miladiyya.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun farmaki sanatar Abuja, sun tarwatsa taron jam'iyyar ADC

Bayanin hukumar Saudiyya

Hukumar kula da yanayi ta kasar Saudi Arabia ta bayyana cewa wannan lamari abu ne na dabi’a kuma yana faruwa lokaci-lokaci a tsarin ilimin taurari.

Hukumar ta ce daidaituwar rana a saman Ka’aba ba lallai ba ne ta haddasa karin zafi fiye da yadda aka saba ko ake sa ran za a samu.

Saudiyya ta ce tsayawar rana a tsakiyar Ka'aba ba ya nufin za a samu karin zafi
Musulman duniya a yayin aikin hajji Hoto: Haramain
Source: Getty Images

Ta ce yanayi yana sauyawa ne bisa wasu abubuwa da dama kamar yawan danshi a sararin sama, gizagizai, karfin iska da kuma yadda iska ke motsi, ba wai matsayin rana kadai ba.

Mai magana da yawun hukumar, Hussein Al Qahtani, ya ce ana lura da wannan lamari duk shekara a matsayin wani bangare na binciken ilimin taurari na yau da kullum.

Ya kara da cewa duk wata magana da ke danganta lamarin da matsanancin zafi na bukatar karin bayani na kimiyya.

A cewarsa, hukumar na amfani da cibiyoyin lura da yanayi, fasahohin zamani da kuma tsarin hasashen yanayi na zamani domin tabbatar da sahihancin bayanan da take fitarwa.

Kara karanta wannan

"Ni ma na rame": Tinubu ya amince manufofinsa sun jefa ƴan Najeriya a wahala

Saudiyya ta yi gyare-gyare

A baya, mun wallafa cewa mahukuntan Saudiyya sun bayyana sababbin tsare-tsaren da aka bullo da su domin saukaka zirga-zirgar alhazai a lokacin aikin Hajji da Umrah na bana.

Ayyukan sun hada da gyara babbar kofar shiga Makkah, masana’antar Kiswah da kuma cibiyar yankan layya ta Adahi gabanin taruwar Musulman duniya domin aikin ibada a jihar.

Haka nan gwamnatin Saudiyya ta bayyana yadda ta aika naman hadaya zuwa kasashen musulmi 27 a duniya a matsayin tallafin jin kai da kuma taya Musulmai murnar Sallah babba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng