Haɗakar ADC: Ministan Buhari Ya Nuna Sha'awar Neman Takarar Shugaban Ƙasa a 2027

Haɗakar ADC: Ministan Buhari Ya Nuna Sha'awar Neman Takarar Shugaban Ƙasa a 2027

  • Ministan sufuri a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi ya nuna sha'awar neman takara a ADC
  • Amaechi, tsohon gwamnan jihar Ribas ya ce shekaru huɗu kacal zai yi idan aka ba shi damar zama shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa
  • Wannan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan ya fice daga APC, ya kuma koma jam'iyyar haɗaka watau ADC da nufin karawa a 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya ce zai mutunta yarjejeniyar karɓa-karɓa tsakanin Kudu da Arewa idan ya samu dama a zaɓen 2027.

Amaechi, tsohon ministan sufuri ya ce idan ya samu tikitin takara a jam'iyyar haɗaka kuma ya ci zabe a 2027, shekaru huɗu kaɗai zai yi ya sauka daga mulki.

Rotimi Amaechi ya nuna sha'awar neman takara.
Taohon minista, Amaechi ya yi alkawarin mutunta yarjejeniyar karɓa-karɓa Hoto: Rotimi Amaechi
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV a cikin shirin siyasa a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC: Ministan Buhari ya nuna sha'awar takara

A cewarsa, ba zai wuce zango ɗaya a mulki ba matuƙar ya samu dama a 2027, yana mai cewa hakan shi ne masalaha ga ƙasa irin Najeriya.

Lokacin da aka tambaye shi ko zai tsaya takara ne domin yin wa’adi guda idan har jam’iyyar haɗaka watau ADC ta ba shi dama, Amaechi ya ce:

“Kwarai da gaske. Na fa gaya muku. Kun san cewa ina faɗar abin da ke zuciyata. Idan ba zan wuce shekara huɗu ba, zan faɗa. Idan kuwa zan wuce shekara huɗu, zan faɗa, bana ɓoye-ɓoye.

Yadda tsarin karɓa-karɓa yake a Najeriya

A Najeriya ana bin wata yarjejeniya da ba a rubuta ba, wadda ke tsara yadda za a rika karɓa-karɓa tsakanin Arewa da Kudu, inda ake sauya shugaban ƙasa bayan kowane shekara takwas.

Shugaba Bola Tinubu daga Kudu maso Yamma ya karɓi mulki a 2023 daga hannun tsohon Shugaba Muhammadu Buhari daga Arewa maso Yamma, wanda ya kammala shekara takwas a ofis.

Yayin da Najeriya ke shirin zaɓen 2027, tattaunawa kan batun tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu ya mamaye harkokin siyasa, rahoton Vanguard.

Duk da sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa ta manyan 'yan siyasa ta fara ƙarfi, ba a bayyana yankin da za a miƙa takarar shugaban ƙasa a cikinta ba tukuna.

Amaechi yana son takara a 2027.
Amaechi ya buƙaci a mutunta yarjejeniyar karba karba tsakanin Kudu da Arewa Hoto: Rt. Hon. Chibuike R Amaechi
Asali: Facebook

Amaechi ya buƙaci a mutunta tsarin karɓa-karɓa

Amma lokacin da aka tambayi Amaechi game da matsayin ADC kan tsarin karɓa-karɓa da yiwuwar tsaida ɗan Kudu wanda zai yi shekara huɗu kacal, sai ya ce:

"Tabbas, tabbas. Bari na gaya muku dalilin haka. A halin da Najeriya ke ciki yanzu, dole ne a kiyaye wannan yarjejeniya, Kudu shekara takwas, Arewa shekara takwas.”

Atiku ya fara kokarin jawo ƴan PDP zuwa ADC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi kira ga ‘yan PDP da su shigo hadakar adawa domin ceto Najeriya.

Atiku, wanda ya kara da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a 2023, ya ce lokaci ya yi da ƴan adawa za su haɗa kai wuri guda domin dawo da martabar ƙasar nan.

Wazirin Adamawa ya yi wannan jawabi a wurin taron magoya bayansa da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262