'Yan Sandan Jihohi: Buba Galadima Ya Hango Rushewar Dimokuradiyya

'Yan Sandan Jihohi: Buba Galadima Ya Hango Rushewar Dimokuradiyya

  • Jigo a NNPP, Buba Galadima ya bayyana fargabar da yake da ita a kan batun kirkirar yan sandan jihohi a Najeriya
  • Buba na ganin samar da ’yan sandan jihohi zai jefa Najeriya cikin haɗari kuma zai iya zama ƙarshen dimokuraɗiyya
  • Ya yi zargin cewa gwamnoni za su mayar da ’yan sandan jiha makamin siyasa don razana wa ko daure abokan hamayya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jigo a jam’iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima, ya fitar da gargaɗi kan yunkurin da wasu shugabannin Najeriya da gwamnoni ke yi na ƙirƙirar ’yan sandan jihohi.

Ya bayyana adawarsa da batun, yana mai cewa wannan mataki barazana ce ga dimokuraɗiyya kuma zai iya kawo karshenta a Najeriya.

Injiniya Buba Galadima da Yan sanda
Buba na adawa da samar da yan sandan jihohi Hoto: Nigeria Police Force/Buba Galadima
Asali: Facebook

A wata hira da ya yi da tashar Arise News, Buba na ganin Najeriya ba ta kai matsayin da za ta iya ɗaukar tsarin ’yan sandan jihohi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya nanata cewa baiwa kowacce jiha ikon kula da jami'an yan sandanta zai fi cutar da al’umma fiye da amfanar su.

Buba: 'Gwamnoni za su addabi yan adawa'

Injiniya Buba ya yi zargin cewa gwamnoni za su mayar da ’yan sandan jiha wata kafa ta danniya, inda za su rika amfani da su wajen razana abokan hamayya.

Ya ce:

“Don Allah, ina roƙon ’yan Najeriya da kuma 'yan Majalisar Tarayya da na jihohi, kada su taɓa amincewa da ƙirƙirar ’yan sandan jiha ko da a wane hali ne.”
“Yanzu muna iya ganin kamar mafita ce, amma idan har hakan ya koma doka, sai ya gagari kowa . Zai hallaka dimokuraɗiyya."

Buba ya soki wasu daga cikin gwamnoni

Jigon NNPP ya ce a mafi yawan jihohi, gwamnoni ne ke canja sakamakon zaben kananan hukumomi a maimakon a bar jama'a su zabi wanda suke so.

Jigo a NNPP, Injiniya Buba Galadima
Buba na fargabar gwamnoni za su ci zarafin jama'a da yan sandan jihohi Hoto: Kwankwasiyya reporters
Asali: Facebook

Ya ce samar da yan sandan jihohi zai iya jawo karuwar lalacewar lamarin ya zama sai abin da suka ga dama ne zai faru

Buba ya ce:

“Idan suka samu dama da makamin ’yan sandan jiha, dimokuraɗiyyar da muke tinkaho da ita za ta lalace. A duk lokacin da na shiga tarukan tsara kundin tsarin mulki — daga na 1987, zuwa na 1994, har zuwa na 2014 karkashin Jonathan — na tsaya tsayin daka kan hana ƙirƙirar ’yan sandan jiha.”

Dangane da muhawarar da ake yi a yanzu kan sauya kundin tsarin mulki, Galadima ya bayyana cewa ba lallai bane a sake doka.

Yana ganin abin da ya fi muhimmanci shi ne sauyin halayen shugabanni da hukumomi.

Buba ya magantu kan sauya shekar Kwankwaso

A wani labarin, mun wallafa cewa Buba Galadima, na ganin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, shi ne ya fi dacewa da shugabancin Najeriya.

Galadima ya bayyana cewa ƙaunar da jama’a ke nunawa Kwankwaso ba ta samo asali daga kuɗi ba, sai dai saboda nagarta da cancantar da ya nuna a baya.

Buba Galadima ya ƙara da cewa Kwankwaso yana da tsari, hangen nesa da basira da za su iya sauya salon tafiyar da mulkin Najeriya da ke fama da ƙalubale iri-iri.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.