Saukar Ganduje: Rikici Ya Barke a APC a Kano, Jam'iyyar NNPP Ta Yi Magana

Saukar Ganduje: Rikici Ya Barke a APC a Kano, Jam'iyyar NNPP Ta Yi Magana

  • Rikici ya kunno kai a APC a jihar Kano bayan saukar Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam’iyya a matakin ƙasa
  • Ƴan jam’iyyar na kira da a sauke shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas bisa zargin neman wa’adin shugabanci karo na uku
  • A daya bangaren, jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar ta musanta cewa da hannunta a rikicin, tana zargin APC da kokarin jefa mata laifi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekara hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A sabuwar dambarwa da ta sake kunno kai a jam’iyyar APC a Kano, ƴan jam’iyyar sun fara matsin lamba kan shugaban jihar, Abdullahi Abbas, da ya ajiye muƙaminsa.

Wannan rikici na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan saukar Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC na ƙasa.

Ana neman shugaban APC a jihar Kano ya sauka
Ana neman shugaban APC a jihar Kano ya sauka. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Facebook

BBC Hausa ta yi rahoto kan yadda lamarin ke shirin tayar da ƙurar sabuwar fargaba a cikin jam’iyyar APC a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan APC na son Abdullahi Abbas ya sauka

Ƙungiyoyi biyu da suka haɗu ƙarƙashin sunan 'APC kadangaren bakin tulu' da 'Ƴan Takwas', sun ce lokaci ya yi da za a canza shugabanci a jihar.

Jagoran ƙungiyar, Nura Na’annabi, ya ce Abdullahi Abbas ya kammala wa’adinsa na shugabanci, amma yana shirin neman wa’adi karo na uku wanda ya saɓa da tsarin jam’iyyar APC.

Na’annabi ya ce:

“Akwai kuma zarge-zargen gazawa a shugabanci da rashin kyawawan kalamai da suka janyo baraka a cikin jam’iyya.”

Sun kuma gabatar da takarda zuwa ga shugaban riko na jam’iyyar APC na ƙasa domin neman a dakatar da Abdullahi Abbas daga shugabanci.

Martanin 'yan bangaren Abdullahi Abbas

Masu goyon bayan Abdullahi Abbas, musamman Sale Kala Kawo, sun karyata zargin, suna masu cewa wannan wani yunƙuri ne da ‘yan Kwankwasiyya ke yi don tayar da hankali a cikin APC.

Sale ya ce:

“Ɗaya daga cikin kungiyoyin ma sun kirasu da ‘kadangaren bakin tulu’, suna cikin jam’iyya kuma suna zagon ƙasa domin neman abin duniya daga gwamnatin jihar.”

Ya kara da cewa babu wani daga cikin masu sukar Abdullahi Abbas da ke da hurumin sauke shi, domin jam’iyyar APC ta fi karfin hakan.

Shugaban APC na Kano tare da Bola Tinubu
Shugaban APC na Kano tare da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: UGC

NNPP ta nisanta kanta daga rikicin APC

A nata bangaren, jam’iyyar NNPP da ke mulki a jihar Kano ta ce bata da hannu a cikin rikicin da ke faruwa a APC.

Wani jigo a NNPP, Ali Muhammad Bichi, ya ce:

“APC na cikin zaman makoki tun daga lokacin da aka sauke jagoransu. Wannan bakin cikin ne ke damunsu, amma kada su daura mana laifi.”

APC ta ce za ta yi nasara a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa mai magana da yawun APC a matakin kasa, Bala Ibrahim ya ce ba su damu da hadakar 'yan adawa a ADC ba.

Bala Ibrahim ya ce yana da tabbacin za su yi nasara a zaben 2027 domin jam'iyyar APC ce ke da goyon bayan 'yan Najeriya.

Mai magana da yawun APC ya yi magana ne bayan manyan 'yan adawa su fara haduwa a ADC domin kalubalantar Bola Tinubu a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng