El Rufa'i Ya Fadi Yadda za a Fafata tsakanin Talakawa da APC a Zaben 2027

El Rufa'i Ya Fadi Yadda za a Fafata tsakanin Talakawa da APC a Zaben 2027

  • Tsohon gwamna jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce babu wata hanya da Shugaba Bola Tinubu zai bi don komawa mulki
  • Ya ce 'yan Najeriya sun gaji, kuma gano duk yan siyasar da ke sauya sheka zuwa APC yanzu ba masoyansu ba ne na hakika
  • El-Rufai wanda ya bar ofis a 2023, ya yi hasashen abin da zai faru a zaben 2027 da yawancin 'yan siyasa ke shiri a kai tun yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna kuma jigo a jam’iyyar SDP, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana cewa gwamnatin APC tana cikin matsala a zabe mai zuwa.

Ya bayyana cewa babu wani ɗan Najeriya da zai sake zaben Bola Ahmed Tinubu, yana mai caccakar ‘yan siyasa da ke komawa jam’iyya mai mulki.

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i da Bola Tinubu
El Rufa'i ya ce babu mai sake zaben Bola Tinubu Hoto: Nasir El-Rufai/@U_Rochas
Asali: Facebook

A cikin wani bidiyo da Chuks ya wallafa a shafin X, El-Rufa’i ya bayyana cewa sauya sheƙar da wasu ‘yan siyasa ke yi na son zuciya ne kawai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa dukkanin wadanda ke rungumar APC ba su da alkibla, kuma suna yi ne saboda fitar su.

Nasir El-Rufa’i ya soki yan adawa

A wani faifan bidiyo da Arc Uche Rochas ya wallafa a shafinsa na X, El-Rufa’i ya ce akwai aji biyu na ‘yan siyasa da ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i
El Rufa'i ce yan Najeriya ne za su fafata da APC a zaben 2027 Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa:

"Duk wanda yake zaton 'yan Najeriya za su sake zaben Bola Tinubu, yana wata ƙasa ne ba Najeriya ba."
"Babu yadda za a yi a sake zaben Bola Tinubu a Najeriya, ban ga ta hanyar da zai koma ba, ko da kuwa 'yan adawa ba su tattara kawunansu ba.
"Na ji dadin yadda ake sauya sheka, saboda ba 'yan Najeriya ne ke sauya sheka ba."

Sauya sheƙa: El-Rufa’i ya soki 'yan siyasa

El-Rufa’i ya jaddada cewa yawancin ‘yan siyasa da ke shiga cikin APC ba su yi hakan ne saboda al’umma ba, illa kawai don kare kansu daga matsaloli.

Ya ce:

"Mayunwatan 'yan siyasa masu neman kwangila, mukamai da kudi ne su ke sauya sheka."
"Sai kuma wadanda suka san Hukumomin EFCC da ICPC za su tuhume su. Sun san sun aikata ba daidai ba, kuma za a iya amfani da hukumomin wajen hana su sakat."

El-Rufa’i ya ce zaben 2027 ba tsakanin jam’iyyun adawa ba ne, sai dai tsakanin gwamnatin Tinubu da al’ummar Najeriya saboda jama'a sun gaji.

"Muna ganin zaben 2027 zai zama tsakanin APC da 'yan Najeriya ne."

Kalaman El-Rufa'i sun ta da kura

A baya, mun wallafa cewa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Ministan ya kara da bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai sauka daga mulki ba har sai ya kammala wa’adinsa na biyu.

Wannan na zuwa ne a matsayin martani ga kalaman tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya ce a 2027 za su mayar da Tinubu Legas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.