Ajiye Shettima: Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Tinubu zai Sanar da Mataimaki a 2026
- Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu ba zai bayyana wanda zai kasance mataimakinsa a 2027 ba sai bayan ya karɓi takarar jam’iyyar a 2026
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce yin hakan yana cikin tsarin mulki, kuma babu matsala tsakanin Tinubu da Kashim Shettima
- Bayo Onanuga ya ce jita-jitar cewa za a ajiye Sanata Kashim Shettima sun samo asali ne daga zato da maganganu marasa tushe balle makama a fadin kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta ce Bola Ahmed Tinubu ba zai bayyana sunan wanda zai tsaya masa takara a matsayin mataimaki a zaben 2027 ba a yanzu.
Rahoto ya nuna cewa sai bayan taron jam’iyyar APC da za a gudanar a shekarar 2026 Bola Tinubu zai ayyana abokin takarar shi.

Asali: Facebook
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanin na zuwa ne a lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan rashin bayyana sunan Kashim Shettima a batun goyon bayan sake fitowa takara da wasu kungiyoyi ke yi wa Tinubu.
“Babu dalilin saurin bayyana mataimaki” — Onanuga
Yayin da aka masa tambaya game da wanda zai yi takara tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a 2027, Onanuga ya ce:
“Idan aka duba tsarin mulki, za a ga cewa sai an zabi dan takara kafin a zabi wanda zai zamo mataimakinsa.
"Wannan ne abin da Buhari ya yi a baya. Tinubu zai zaɓi mataimakinsa bayan an tabbatar da shi a taron jam’iyya.”
Akwai matsala tsakanin Tinubu da Shettima?
Onanuga ya ce babu wani rikici ko rashin jituwa tsakanin shugaban ƙasa da mataimakinsa, Shettima. Ya ce dukkanin rade-radin da ake yadawa ba su da tushe.
Ya kara da cewa:
“Wasu ma har suna cewa ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, shi ne mataimaki, wanda wannan magana ce maras tushe. Jama’a su daina kirkirar labarai da babu su,”

Asali: UGC
Martani kan sukar da jam’iyyun adawa ke yi
A karshe, Onanuga ya bayyana cewa goyon bayan da wasu kungiyoyi ke bai wa Tinubu, duk da cewa INEC ba ta buɗe lokacin yaƙin neman zaɓe ba, martani ne ga yunkurin jam’iyyun adawa.
Onanuga ya ce:
“Sun fara maganar siyasar 2027, ba za mu zauna muna kallo ba. Dole mu nuna cewa ba mu yi barci ba. Wannan ne ya sa muke maraba da goyon bayan,"
An radawa asibiti sunan Tinubu a Kaduna
A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto muku cewa gwamnatin Uba Sani ta bude asibitin Bola Ahmed Tinubu a Kaduna.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa sun bude asibitin da sunan Bola Tinubu domin girmama shugaban kasar.
A yayin bude asibitin, Sanata Uba Sani ya roki Bola Tinubu ya kammala wani sashen da bai kammala ba, kuma nan take shugaban ya yarda da bukatar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng