Kwankwaso: Abin da Ya Dace 'Yan Sanda da Gwamnati Su Yi kan Batan Dadiyata
- Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya buƙaci a tabbatar da adalci kan ɓacewar Abubakar Idris Dadiyata
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya yabawa sabon binciken da sufeton ‘yan sanda ya bayar da umarni a yi kan lamarin da ya dawo danye
- Sanata Kwankwaso ya nemi gwamnati ta tallafa wa Dadiyata da iyalansa idan bincike ya tabbatar yana raye, sannan a bi masa hakkinsa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya maraba da matakin da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu.
Sufeton yan sanda ya bayar da umarnin sake buɗe bincike kan ɓacewar ɗan gwagwarmaya, Abubakar Idris Dadiyata.

Source: Facebook
A sakon da ya fitar, wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Kwankwasi ya tuno yadda aka sace Dadiyata a jihar Kaduna tun a shekarar 2019, kuma har yanzu ba a gano inda yake ba.
Kiran Kwankwaso game da bincike kan Dadiyata
A rahoton jaridar Daily Post, Kwankwaso ya yi martani ne bayan rahotanni sun bayyana cewa wani tsohon mataimaki ga tsohon gwamna ya ballo ruwa.
Musa Muhammad Kamarawa, ya bayar da shaida cewa wani jami’in ‘yan sanda ne ya bindige Dadiyata da wani Saminu S/Fada Gusau a gaban shi.
A kan wannan batu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce tun bayan sace Dadiyata yake bibiyar lamarin da matuƙar damuwa.
Ya ce:
“Na samu labarin sabuwar shaidar da wani tsohon mataimaki ga tsohon gwamnan jiha ya bayar, inda ya yi zargin cewa wasu jami’an ‘yan sanda sun ɗauki alhakin ɓacewar Abubakar Idris Dadiyata a Kaduna.”
Kwankwaso ya ƙara da cewa shi da abokan aikinsa sun daɗe suna kira da a yi cikakken bincike domin hukunta masu hannu a lamarin.

Source: Facebook
Ya ce:
“Tun bayan sace shi a shekarar 2019, ni da abokan aikina muna ci gaba da addu’a tare da kira ga hukumomi su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a ɓacewarsa.”
Kwankwaso ya bukaci a yi tsaftataccen bincike
Tsohon gwamnan Kano ya bayyana umarnin da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ya bayar na sake gudanar da bincike a matsayin mataki mai kyau duk da cewa ya ce an daɗe ana jiran hakan.
A cewarsa:
“Abin ƙarfafa gwiwa ne ganin cewa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari. Ina yabawa Sufeto Janar saboda wannan mataki mai muhimmanci da aka daɗe ana jira.”
Kwankwaso ya kuma buƙaci jami’an tsaro su sanya ido sosai kan mutanen da aka ambata a cikin shaidar domin hana duk wani yunƙuri na kawo cikas ga binciken.
Haka kuma ya roƙi gwamnati ta tabbatar da cewa idan binciken ya nuna Dadiyata yana raye, shi da iyalansa sun samu tallafi da diyya saboda wahalhalun da suka sha tsawon shekaru.
Kwankwaso ya kuma yaba wa jama’a da lauyoyi musamman Barrista Abba Hikima Fagge saboda ci gaba da neman gaskiya kan lamarin.
El-Rufa'i ya magantu kan Dadiyata
A baya, mun wallafa cewa tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya musanta hannun gwamnatinsa a batun batan Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.
El-Rufai ya bayyana cewa bincike ya nuna jami'an tsaro daga Kano aka aiko domin sace Dadiyata daga gidansa dake Kaduna, amma babu ruwan gwamnatinsa a lamarin.
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa shi bai ma ma san Dadiyata ba har sai da aka sace shi, don haka a tuhumi gwamnatin Kano na wancan lokaci a karkashin Abdullahi Ganduje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


