Sabon Sabani Ya Bulla APC, Ana Zargin 'Yan Jam'iyya da Yi wa PDP Aiki
- Jam’iyyar APC a jihar Oyo ta bayyana shirin hukunta duk wani memba da aka samu da hannu a aikata ayyukan cin amanar jam’iyya
- Hakan na zuwa ne bayan wasu shugabannin jam’iyyar biyu sun yabawa gwamnatin PDP ta gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo
- APC ta ce ba za ta sake lamuntar cin amanar jam’iyya da rashin da’a ba, tana mai cewa duk mai kokarin dagula tafiyar jam’iyyar zai fuskanci hukunci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Jam’iyyar APC a Jihar Oyo ta fitar da sanarwa mai cike da gargadi, inda ta ce za ta dauki matakin ladabtarwa kan duk wani mamba da aka samu da hannu a cin amanar jam’iyya.
Sanarwar na zuwa ne bayan wasu rahotanni na kafafen yada labarai sun nuna cewa wasu shugabannin APC biyu sun nuna goyon baya ga gwamnatin PDP ta Gwamna Seyi Makinde.

Asali: Twitter
Tribune ta wallafa cewa mai magana da yawun jam’iyyar, Olawale Sadare, ne ya fitar da sanarwar a garin Ibadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta yi barazanar hukunta 'ya'yanta a Oyo
A cewar Sadare, saba wa jam’iyya da rashin da’a sun dade suna dagula tafiyar APC a jihar, yana mai cewa yanzu lokaci ya yi da za a tashi tsaye domin kare martabar jam’iyyar.
The Nation ta wallafa cewa ya ce:
“Ban da son zuciya da rashin tarbiyya, babu dan jam’iyyar kirki da zai rika yawo yana yabon gwamnatin PDP da ke barnatar da dukiyar jama’a tsawon shekaru shida da suka wuce.”
Sadare ya ce tuni jam’iyyar ta gaji da cin amanar wasu da ke rura wutar rikici, kuma shugabannin jam’iyyar za su dauki matakin ladabtarwa ba tare da wani rangwame ba.

Asali: Facebook
APC ta gano masu yi wa PDP aiki a jihar Oyo
Sadare ya kara da cewa binciken da jam’iyyar ta gudanar ya tabbatar da cewa wasu da ke kiran kansu dattawan APC sun yi aiki wa PDP kwanan nan ba tare da wani dalili na kwarai ba.
Duk da haka, ya ce jam’iyyar za ta saurari wadannan mutane idan akwai yiwuwar a fahimtar da su kuskurensu.
Ya ce:
“Duk wani mamba na gaskiya ya kamata ya tsaya tsayin daka kan samun nasara, wanda ke nufin tabbatar da nasarar APC a gaba daya Jihar Oyo a zabe mai zuwa.”
Jam'iyyar APC ta nemi hadin kai a jihar Oyo
Kakakin jam'iyyar ya ce shugaban APC na jihar, Olayide Abas, da sauran shugabanni sun yi aiki tukuru wajen sasanta rikice-rikice da kuma tabbatar da zaman lafiya a cikin jam’iyyar.
Sanarwar ta ce da dama daga cikin fitattun ’yan siyasa a jihar sun fara komawa APC, wanda hakan ke nuna jam’iyyar na samun karbuwa.
Sadare ya gargadi duk wani dan jam’iyya da ke kokarin karya wannan gini da aka kafa cewa za a dauke shi tamkar makiyi, kuma ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta shi.
PDP ta rama maganar da Tinubu ya fada mata
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta rama bakar maganar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mata a ranar dimokuradiyya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi magana a ranar dimokuradiyya yana cewa yana farin ciki da rikicin da PDP ke fama da shi.
Bayan rikicin APC da ya faru a Gombe da aka yi kokarin kai farmaki ga Abdullahi Ganduje, PDP ta ce ita ma ta ji dadin lamarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng