'An Karya Ka'ida,' INEC Ta Jawo wa PDP Sabuwar Matsala kan Taron NEC

'An Karya Ka'ida,' INEC Ta Jawo wa PDP Sabuwar Matsala kan Taron NEC

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi watsi da sanarwar taron kwamitin zartaswa na kasa na PDP karo na 100
  • Wasikar da mukaddashiyar sakatariyar INEC, Hajiya Hau’ru Aminu ya fitar ta bayyana cewa jam'iyyar ba ta bi tsarin dokar hukumar ba
  • A takardar sanarwar da PDP ta aika wa hukumar zaben, ta sanar da cewa ta shirya gudanar da babban taronta a ranar 30 ga watan Yuni

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta yi watsi da sanarwar da jam’iyyar PDP ta aika mata dangane da taron kwamitin zartaswa na kasa (NEC) karo na 100 da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga Yuni, 2025.

Wata wasika da Hajiya Hau’ru Aminu ta rattaba wa hannu, wacce ta bayyana kanta a matsayin mukaddashiyar sakatariyar INEC, ta bayyana matsayar hukumar tare da nuna cewa an karya doka.

Mukaddashin shugaban PDP, Ambasada Umar Iliya Damagum
INEC ta yi watsi da sanarwar PDP na gudanar da taron NEC Hoto: Auwal Musa Muhammad Kaska
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa INEC ta ce wasikar sanarwar ba ta cika sharuddan da aka shimfida ba, musamman sashen 2(12)(3) na dokokin 2022 da aka tanada don jagorantar jam’iyyun siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Damagum ya aika wasika ga hukumar INEC

Channels ta ruwaito PDP ta aikewa INEC wasika don sanar da shirinta na gudanar da taron NEC na karo na 100 a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Sanarwar ta samu sa hannu daga mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Umar Damagum kadai.

Sanarwar, wacce aka rubuta a ranar 30 ga Mayu, ta zo bisa buƙatar da doka ta gindaya cewa dole ne jam’iyyu su sanar da INEC akalla kwana 21 kafin gudanar da taron NEC.

INEC ta yi watsi da sanarwar jam'iyyar PDP

Sai dai INEC ta ce wannan sanarwa ba ta da inganci saboda ba shugaban jam’iyyar da sakataren jam’iyyar suka rattaba hannu a tare ba, kamar yadda doka ta bukata.

INEC ba ta amince da sanarwar taron PDP ba
INEC ta ce PDP ta karya ka'ida Hoto: Hoto: Auwal Musa Muhammad Kaska
Asali: Twitter

A cikin wasikar da INEC ta aika wa PDP, hukumar ta ce:

“Hukumar na jawo hankalinku cewa wannan sanarwa ba ta yi daidai da sashen 2(12)(3) na Dokokin da Ka’idojin Jam’iyyun Siyasa, 2022 ba, wanda ke cewa ‘dole ne shugaban jam’iyya na kasa da Sakataren jam’iyya na kasa su hada hannu wajen sanya hannu a sanarwar kiran taron gangami, taron wakilai, ko wani taro da za a tura wa Hukumar.’ Ku kiyaye wannan.”

Idan za a iya tunawa, taron NEC na karo na 99 da PDP ta shirya a baya ma ya fuskanci tsaiko, bayan Hukumar Raya Birnin Tarayya ta rufe hedikwatar jam’iyyar kasa da awanni 24 kafin taron.

Gwamna ya magantu kan barin PDP

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya yi watsi da jita-jitar da ke yawo cewa yana shirin barin jam’iyyar PDP domin komawa jam’iyyar APC dake mulkin kasa.

Gwamna Mutfwang ya bayyana jita-jitar a matsayin ƙarya marar tushe, yana mai cewa PDP ce ginshiƙin siyasar Filato, kuma barin jam’iyyar zai zama cin amana ga al’ummar da suka zabeshi.

Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta samun sauya sheƙar wasu gwamnoni daga PDP zuwa APC, ciki har da gwamnonin Delta, Sheriff Oborevwori, da Akwa Ibom, Umo Eno.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.