Ana Kokarin Yin Sulhu, Wata Tawaga Ta Musamman Dauke da Sakon Amurka Ta Isa Iran
- Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya karbi tawagar Pakistan a birnin Tehran yau Laraba, 15 ga watan Afrilu, 2026
- Tawagar Pakistan karkashin jagorancin babban hafsan tsaron kasa, Janar Asim Munir ta isa Iran ne dauke da wani sako daga Amurka
- Bayanai sun nuna cewa wannan ziyara wani bangare ne na kokarin da Pakistan ke yi don sake hada Amurka da Iran a teburin tattaunawa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Wata tawaga ta musamman daga kasar Pakistan ta isa birnin Tehran domin tattaunawa kan yadda za a koma zagaye na biyu na zaman sulhu tsakanin Iran da Amurka.
Majiyoyin Iran sun shaida cewa babban hafsan rundunar sojin Pakistan, Janar Asim Munir ne ya jagoranci tawagar zuwa birnin Tehran na kasar Musulunci ta Iran yau Laraba.

Source: Getty Images
Ministan Iran ya karbi tawagar Pakistan
Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya karɓi wannan babbar tawaga daga Pakistan ƙarƙashin jagorancin babban hafsan sojin ƙasar, Janar Asim Munir.
Rahotanni sun nuna cewa wannan tawaga ta Pakistan ta je Iran ne domin mika sƙo daga Amurka, tare da duba hanyoyin da za a bi wajen fara sabon zagaye na tattaunawar sulhu.
Sashen yaɗa labarai na rundunar sojin Pakistan ya bayyana cewa Ministan harkokin cikin gida na ƙasar, Mohsin Naqvi, ma cikin tawagar da ta kai ziyara Tehran, innji rahoton NBC News.
Ana ci gaba da tattaunawa ta hannun Pakistan
Iran ta tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa ta hannun Pakistan, bayan zagaye na farko na ganawar kai tsaye da Amurka a Islamabad ya kare ba tare da cimma wata matsaya ba a ƙarshen makon da ya gabata.
Wannan yunƙurin diflomasiyya na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya nuna yiwuwar yin sulhu, inda ya bayyana cewa akwai yiwuwar kawo ƙarshen rikicin kasarsa da Iran cikin kankanin lokaci.
Haka kuma, Trump ya bayyana cewa akwai yiwuwar tawaga daga Amurka za ta sake komawa Pakistan, yana mai yaba wa Janar Munir kan rawar da yake takawa wajen sasanta rikicin.

Source: Getty Images
A halin yanzu, akwai yarjemeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu tsakanin Amurka da Iran, wanda ake sa ran za ta ƙare ranar 22 ga Afrilu.
Kasar Pakistan na ƙoƙarin ganin an samu matsaya kan muhimman batutuwa uku da suka hana cimma yarjejeniya a taron Islamabad, waɗanda suka haɗa da shirin nukiliyar Iran, buɗe mashigar ruwa ta Hormuz da biyan diyya ga Iran.
Iran ta aika sako ga kasashen Turai
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi wata tattaunawa mai matukar muhimmanci da takwaransa na kasar Faransa, Emmanuel Macron.
Shugaba Pezeshkian ya tabo batun yadda za a kawo karshen yakin kasar Iran da Amurka yayin wannan tattaunawa da ya yi Macron ta wayar tarho ranar Litinin da ta wuce.
A cewarsa, akwai bukatar kungiyar Tarayyar Turai ta sa baki kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen wannan yaki na Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng

