Gwamna Bala Ya Sake Saɓawa Shugaba Tinubu, Ya Yi Magana Mai Zafi kan 'Jam'iyya 1'

Gwamna Bala Ya Sake Saɓawa Shugaba Tinubu, Ya Yi Magana Mai Zafi kan 'Jam'iyya 1'

  • Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya sake yin maganar da ta ci karo na kalaman shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Sanata Bala ya yi gargaɗin cewa matuƙar ba a ɗauki matakin da ya dace ba, Najeriya na iya komawa tsarin jam'iyya ɗaya
  • Gwamna Bala, wanda shi ne shugaban gwamnonin PDP, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su tashi tsaye, su kare tsarin dimokuraɗiyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed (Ƙauran Bauchi), ya nuna damuwa kan yadda aka fara juya tsarin siyasa a Najeriya.

Gwamna Bala ya yi gargaɗin cewa ƙasar na iya fada tsarin jam’iyya ɗaya kafin zaɓen 2027 idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.

Gwamna Bala Mohammed na Bauchi.
Gwamnan Bauchi ya sake saɓawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Senator Bala Mohammed
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin wakilinsa, Mohammed Atiku Isah, a wurin taron tunawa da ranar dimokuraɗiyya a Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar matasa ta Young Democrats of Nigeria ce ta shirya taron a Kaduna, mai kuma.ta gayyaci shugaban gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.

Da yake jawabin ranar dimokuraɗiyya a gaban Majalisar Tarayya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya musanta cewa gwamnatinsa na kokarin mayar da Najeriya ƙasar da jam’iyya ɗaya ke mulki.

Kalaman Gwamna Bala sun saɓa da na Tinubu

Sai dai Gwamna Bala ya jaddada cewa dole ne a kare tsarin siyasar Najeriya daga yunƙurin mamayar wata jam’iyya guda ɗaya tak.

A cewarsa, darasin da ke cikin ranar 12 ga Yuni na 1993 shi ne haɗin kai da ƙawance, da kuma tuna sadaukarwar da aka yi domim fuskantar kowane irin ƙalubale.

"Yan adawa na fuskantar barazana, kuma akwai hadari babba idan aka maida Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya kafin 2027.
"Wannan lamari na cutar da ginshiƙan dimokuraɗiyya wanda aka gina bisa adalci, ɗimbin bambancin da ke cikin ƙasa, da gasa tsakanin jam’iyyu,” in ji shi.

Gwamna Bala ya koka kan matsin rayuwa

Ƙauran Bauchi ya bayyana cewa cire tallafin mai da lalata tsarin musayar kuɗi da kuma tsadar rayuwa sun jefa al’umma cikin wahala mara misaltuwa.

“Wannan na nuna rashin fahimtar wahalhalun talakawa. Dole gwamnatin tarayya ta saurari ra’ayin jama’a, ta sake nazarin manufofinta,” in ji Gwamna Bala.

Ya kuma jaddada cewa ma’ana da darasin da ke cikin ranar 12 ga Yuni bai tsaya kan siyasa kawai ba, har da adalcin da walwalar jama'a, rahoton Vanguard.

Gwamna Bala da Shugaban Kasa, Bola Tinubu.
Gwamna Bala ya buƙaci gwamnatin Tinubu ta sake nazari kan manufofinta Hoto: Senator Bala Mohammed, @OfficialABAT
Asali: Facebook
“Dimokuraɗiyya na nufin haɗin kai, adalci na tattalin arziƙi da raba albarkatu yadda ya kamata, ba wai siyasar da ke ƙara nesanta tsakanin gwamnati da talakawa ba," in ji shi.

Gwamna Bala ya ƙarƙare da kira ga 'yan Najeriya da su zama masu lura da kare darajar dimokuraɗiyya kuma su tashi tsaye wajen kare ’yancinsu.

Minista ya faɗi saɓaninsa da Kauran Bauchi

A wani labarin, kun ji cewa ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar ya bayyana rikicin da ya kusa haɗa shi faɗa da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi.

Tuggar ya tabbatar da cewa ya sami saɓani da Gwamna Bala a gaban mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima lokacin da ya kawo ziyara a Bauchi.

Ya nanata cewa gwamnan Bauchi ne ya fara takalo shi, har da zagin mahaifinsa kuma ya yi ikirarin zai gaura masa mari a cikin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262