Hisbah Ta Kama Kwarto a cikin Jakar ‘Ghana Must Go’ a Dakin Matar Aure

Hisbah Ta Kama Kwarto a cikin Jakar ‘Ghana Must Go’ a Dakin Matar Aure

  • Jami’an Hisbah a Kebbi sun kai samame gidan wata matar aure a Birnin Kebbi inda aka yi ram da wani mutum da aka samu ya ɓoya a gidanta
  • Mazauna unguwar Badariya ne suka sanar da Hisbah bayan sun ga mutumin ya shiga gidan matar da dare, lamarin da ya jawo zargin lalata
  • Hisbah ta ce mutumin da matar sun amsa zargin soyayya tsakaninsu, kuma za a gurfanar da su a kotu ƙarƙashin dokar Musulunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin Kebbi, Jihar Kebbi - Jami’an Hisbah ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Addini ta Kebbi sun kama wani mutum da ake zargin kwarto ne.

Hukumar Hisbah ta yi nasarar kama mutumin da aka samu ya ɓoye cikin jakar 'Ghana Must-Go' a gidan matar aure.

Hisbah ta kama kwarto a dakin matar aure
Taswirar jihar Kebbi da Hisbah ta kama kwarto a gidan matar aure. Hoto: Legit.
Source: Original

Daraktan Shari’a na hukumar, Sirajo Kamba, ya tabbatar da kama mutumin cikin wata sanarwa da aka fitar wanda Daily Trust ta samu a ranar Talata 19 ga watan Mayun 2026 a Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Duk da ƙaryata Amurka, an tabbatar da hannun Trump a hallaka jagoran ISIS a Najeriya

An kama mutumin ne a gidan wata matar aure da ke yankin Badariya a Birnin Kebbi bayan mazauna yankin sun kai rahoto ga Hisbah

Kamba ya ce mazauna yankin sun sanar da Hisbah da misalin ƙarfe 12:15 na dare bayan sun ga wani mutum ya shiga gidan matar.

Mazauna yankin sun yi zargin cewa akwai alaƙar da ta saɓa wa koyarwar Musulunci, lamarin da ya sa suka sanar da hukumomi.

Bayan samun rahoton, hukumar Hisbah ta Kebbi ta tura jami’anta cikin gaggawa domin gudanar da bincike a gidan matar da ake zargi.

Da jami’an suka isa gidan, sun nemi izinin bincike amma matar ta fara musanta cewa babu wani mutum a cikin gidan nata.

Daga baya matar ta amince a bincika gidan, inda jami’an suka gano mutumin a ɓoye cikin wani jakar 'Ghana Must-Go' a ɗakin gidan.

Kamba ya ce ƙarin bincike ya nuna akwai alaƙar soyayya tsakanin mutumin da matar aure, abin da ya jawo ci gaba da bincike.

Ya ƙara da cewa yayin tambayoyi, mutumin da matar sun amsa zargin da ake yi musu na shiga alaƙar soyayya ta ɓoye.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kafa tarihi, ya kirkiri sabon ofishi a fadar shugaban kasa kan tsaro

Hukumar Hisbah ta bayyana cewa za a gurfanar da mutanen biyu a kotu domin fuskantar hukunci ƙarƙashin dokar Musulunci a jihar Kebbi.

Ya ƙara da cewa yayin tambayoyi, mutumin da matar sun amsa zargin da ake yi musu na shiga alaƙar soyayya ta ɓoye.

Hisbah ta kama ango da amarya a Kano

Mun ba ku labari a baya cewa Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama matasa biyar bisa zargin yin aure ba tare da amincewar iyaye ba.

Rahoto ya ce cikin wadanda aka kama akwai amarya, ango, da wasu uku da suka shiga wajen shaidar daura auren ba tare da bin ka'ida ba.

Hisbah ta byyana cewa an yi auren ne da sadaki na ₦10,000 wanda bai kai ka’idar da Musulunci ya tanada ba, ta ce hakan ya sa akacafke su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.