Minista Ya Yabi Tinubu, Ya Fadi Abin da Ya Jawowa Najeriya a Idon Duniya
- Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ƙwararo yabo ga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Mohammed Idris ya bayyana cewa daraja da martabar Najeriya ta fara dawowa a idon duniya a ƙarƙashin shugabancin Tinubu
- Ministan ya kuma yaba da matakan da Tinubu ya ɗauka kan farfaɗo da tattalin arziƙi, inda ya ce kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya yabi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Mohammed Idris ya ce Najeriya na sake samun mutunci da daraja a idon duniya ƙarƙashin shugabancin Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Twitter
Mohammed Idris ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi domin bikin ranar dimokuraɗiyya, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Minista ya yabi manufofin Bola Tinubu
Ministan ya ce gyare-gyaren tattalin arziƙi da Shugaba Tinubu ke aiwatarwa na mayar da Najeriya kan hanya madaidaiciya domin samun ci gaba da kuma sake samun muhimmanci a idon duniya.
Ya ce muhimman matakai kamar cire tallafin man fetur da daidaita farashin canjin kuɗi sun kasance matakai masu nuna ƙarfin hali kuma dole ne a ɗauke su domin ceto tattalin arziƙin ƙasar nan.
“Waɗannan matakai sun kasance masu wahala, amma dole ne a ɗauke su."
“Sun janyo tarnaƙi a farko, amma kamar jirgin sama da ke tashi daga ƙasa, yanzu muna kai wa matakin daidaituwa."
- Mohammed Idris
Mohammed Idris ya yi batun dimokuraɗiyya
Ya bayyana cikar shekara 26 da Najeriya ta koma mulkin farar hula a matsayin lokaci na murna da kuma tunani mai zurfi kan tafiyar dimokuraɗiyya da tattalin arziƙin ƙasar nan.
Ministan ya ce kuɗaɗen da aka tanada daga cire tallafin fetur suna tafiya ne zuwa muhimman ayyuka, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, ciki har da hanyoyi masu faɗi guda biyu da suka wuce tsawon kilomita 1,700.
"Manufar ba wai haɗa gari da gari kawai ba ce, amma samar da damarmaki na tattalin arziƙi."
- Mohammed Idris

Asali: UGC
Minista ya yabawa Shugaba Tinubu
Ya ƙara da cewa an sake dawo da martabar Najeriya a idon duniya a ƙarƙashin shugabancin Tinubu.
"Najeriya na dawowa kan turbar da ta dace. Tana koma wa matsayin ƙasa mai muhimmanci a cikin ƙasashen duniya.”
"Mutuncin da Najeriya ke da shi a da, yana dawowa sannu a hankali. Ƴan kasuwa da masu saka hannun jari sun fi samun ƙwarin gwiwa kan ƙasarmu yanzu."
- Mohammed Idris
Tinubu ya magantu kan masu sukarsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan masu sukar gwamnatinsa.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa masu sukar gwamnatinsa ba za su sare masa gwiwa ba wajen gudanar da ayyukan da yake yi a ƙasar nan.
Hakazalika ya kuma shawarci hukumomin tsaro da kada su tsangwami ƴan Najeriya saboda sukar gwamnatinsa, yana mai jaddada kare ƴancin fadar albarkacin bakin da suke da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng