‘A Kai Kasuwa’: Shugaban Croatia Ya Ki Amincewa da Sabon Jakadan Isra’ila a Kasar

‘A Kai Kasuwa’: Shugaban Croatia Ya Ki Amincewa da Sabon Jakadan Isra’ila a Kasar

  • Shugaban ƙasar Croatia, Zoran Milanovic, ya yib fatali da shirin Isra''ila na turo sabon jakada zuwa kasar yayin da ake cikin yaki da Iran
  • Milanovic ya dauki matakin ne kin amincewa ne da hakan saboda manufofin gwamnatin Isra’ila da rikicin diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu
  • Fadar shugaban Croatia ta ce Isra’ila ta karya ƙa’idar diflomasiyya bayan bayyana sunan jakadan kafin samun amincewar shugaban ƙasar a hukumance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Zagreb, Croatia - Shugaban ƙasar Croatia, Zoran Milanovic, ya ƙi amincewa da sabon jakadan Isra’ila saboda abin da ya kira manufofin gwamnatin Isra’ila na yanzu.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar ranar Litinin, ta ce sabon jakadan Isra’ilar ba zai samu amincewar shugaban ƙasar ba.

Croatia ta ki yadda da sabon jakadan Isra'ila
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Marc Israel SELLEM/POOL/AFP, Georgian Presidency/Anadolu.
Source: Getty Images

Sanarwar ta bayyana cewa a baya Croatia ba ta saba yin magana a bainar jama’a kan naɗin jakadu saboda bin ƙa’idar diflomasiyya, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Tsagin jam'iyyar adawa za ta yi bazata, kowa zai samu fom din takara kyauta

Musabbabin watsi da jakadan Isra'ila a Croatia

Sai dai fadar shugaban ƙasar ta ce Isra’ila ta karya wannan ƙa’ida bayan bayyana sunan wanda aka zaɓa kafin samun amincewar hukuma daga Croatia.

Fadar shugaban ta ce saboda matakin da Isra’ila ta ɗauka, shugaban ƙasar ya tabbatar da cewa ba zai amince da jakadan ba.

Ta ƙara da cewa amincewa ko kin amincewa da jakadun ƙasashen waje cikakken haƙƙi ne na gwamnatin Croatia da shugaban ƙasar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa babu wata matsin lambar siyasa ko ta jama’a da za ta sauya matsayar shugaban ƙasar kan batun, kamar yadda Anadolu Ajnasi ya ruwaito.

Sanarwar ta ce:

“Sabon jakadan ƙasar Isra’ila bai samu amincewar shugaban ƙasa ba, kuma ba zai samu wannan amincewar ba.”
An i amincewa da sabon jakadan Isra'ila a Croatia
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a Tel Aviv. Hoto: Taylor Hill.
Source: Getty Images

Wane martani hukumomi a Isra'ila suka yi?

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin Isra’ila ba su fitar da wata sanarwa ko martani kan matakin gwamnatin Croatia ba.

Rahotanni sun ce Nissan Amdur, wanda aka amince da naɗinsa tun watan Nuwambar 2025 domin maye gurbin Jakadan Isra'ila, Gary Koren zai iso ne bayan ƙarshen wa’adin Koren a ƙarshen wannan wata a matsayin chargé d’affaires, mukamin da ba ya buƙatar amincewar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Shugabar ALGON a Kano ta sha da kyar bayan 'yan daba sun far mata

Majiyoyi suka ce ƙin amincewar Milanović da Amdur shi ne karo na farko da shugaban ƙasar Croatia ya ƙi karɓar jakadan wata ƙasa, lamarin da ake kallon sa a matsayin babban saɓani ga ƙa’idar diflomasiyya.

Yahudawa sun kona masallaci a Isra'ila

Mun ba ku labarin cewa wasu ƴan Isra’ila sun kai hari a wani masallaci yayin da suka banka wuta kan motoci da ke harabar wurin ibadar.

Majiyoyi suka ce lamarin ya faru ne a kauyen Jibiya da ke kusa da Ramallah, tare da rubuta kalaman wariyar launin fata a bangon gidaje.

Maharan yahudawa sun kai hari gidajen Falasdinawa a Al-Lubban al-Sharqiya kusa da Nablus, inda suka karya kofofi da firgita mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.