Zargi Ya Dawo kan Zulum: An Taso Gwamna a Gaba bayan Kai Wa Ganduje Hari

Zargi Ya Dawo kan Zulum: An Taso Gwamna a Gaba bayan Kai Wa Ganduje Hari

  • Wata kungiyar APC daga Arewa ta Tsakiya ta bukaci Gwamna Babagana Zulum ya ba da hakuri kan abin da ya faru a Gombe
  • Kungiyar ta zargi Zulum da daukar nauyin'yan daba da suka kai wa Abdullahi Ganduje hari a taron jam'iyyar a jihar Gombe
  • Shugaban kungiyar, Zazzaga ya zargi Zulum da kawo rikici a taron APC, ya ce bai dace ya hana shugaban jam'iyya aikinsa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Kungiyar APC a Arewa ta Tsakiya ta yi Allah wadai da abin da ya faru a jihar Gombe a ranar Lahadi 15 ga watan Yunin 2025.

Kungiyar ta bukaci Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya ba da hakuri bisa zargin daukar ‘yan daba da suka kai wa Abdullahi Ganduje hari.

APC na fara nuna yarda ga gwamna Zulum
Ana zargin Gwamna Zulum kan harin da aka kai wa Ganduje. Hoto: Ganduje Media for Tinubu.
Asali: Facebook

Rigimar Gombe: Kungiyar APC ta zargi Zulum

Shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga, ya bayyana cewa Gwamna Zulum ne ya jagoranci ‘yan daba domin su kai wa Ganduje hari, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta kare Ganduje, tana mai cewa shugaban kasa ne kadai ke da hurumin zabar mataimakinsa a zabe, ba wani mutum ko yankin da zai tilasta shi.

A cewar kungiyar:

“Muna Allah-wadai da yadda Gwamna Zulum ya dauki ‘yan daba domin kai wa Ganduje hari, wanda ke gudanar da aikinsa cikin gaskiya da rikon amana.”

Kungiyar ta ce babu wata hujja da ke sa yankin Arewa maso Gabas ya ji yana da iko a jam’iyyar APC, tun da bai ba da kuri'u da ake tsammani ba a 2023.

A cewar sanarwar, yankin Arewa ta Tsakiya da ya fi kawo wa APC da Tinubu kuri’u ya fi cancanta da samun karramawa a cikin jam’iyyar.

Yan APC sun zargi Zulum kan rigimar jam'iyyar a Gombe
Kungiyar APC ta zargi Zulum kan hari ga Ganduje. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Asali: Original

Ganduje ya yi Allah wadai da lamarin

A bangarensa, hadimin shugaban APC ya bayyana cewa daukar matakin ta da zaune tsaye da tarzoma a taron jam’iyya ba abu bane da za a lamunta ba.

Oliver Okpala ya ce yanzu siyasar Najeriya ba ta da gurbi ga tashin hankali, saboda haka ya kamata ‘yan jam’iyya su rungumi siyasar da kima da kamun kai.

Da yake mayar da martani game da rikicin siyasa a Gombe, ya ce irin wannan rikici ne ya janyo tabarbarewar siyasa a Yammacin Najeriya a baya, Punch ta ruwaito.

Ya ce:

“Muna Allah-wadai da wannan danyen aiki. Ba za a bar Najeriya ta fada cikin tarzoma ba; irin wannan taro ya kamata ya kasance mai kima.”
“Wannan lamari ba shi da amfani ga martabar Najeriya."

APC ta magantu kan rigimar jam'iyyar a Gombe

Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar APC ta zargi wasu 'yan adawa, musamman mabiya tafiyar Kwankwasiyya da yayata hatsaniyar da ta faru da Gombe.

Sakataren yada labaran APC, Ahmed S Aruwa ya ce abin da ya faru ba sabon batu ba ne a siyasa, kuma baya nufin akwai baraka a APC.

Aruwa ya karyata rade-radin da ke cewa Dr. Abdullahi Ganduje na shirin neman kujerar mataimakin shugaban kasa a 2027 domin maye gurbin Kashim Shettima.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.