Tsugune ba Ta Kare ba: Ƴan APC Sun Magantu kan Kujerar Shettima da Ganduje
- Wata kungiyar APC daga Arewa ta Tsakiya ta bayyana goyon bayansa ga shugaba Bola Tinubu da Abdullahi Ganduje
- Kungiyar ta ce Tinubu ne kaɗai zai tsaya takara a 2027, yana da hurumin zaɓar mataimakinsa ba tare da tilastawa ba
- Ta ce abin da ya faru a taron Gombe abin takaici ne, amma APC na ci gaba da kasancewa jam’iyya mai ƙarfi da haɗin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Kungiyar jam’iyyar APC na Arewa ta Tsakiya ta yi magana kan tikitin takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima.
Jam'iyyar APC a yankin ta nuna goyon bayanta ga shugabancin Shugaba Bola Tinubu da kuma Abdullahi Ganduje.

Asali: Twitter
Matsayar APC kan takarar Tinubu da Shettima
Punch ta ce hakan ya faru ne bayan abubuwan da suka faru a taron masu ruwa da tsaki na yankin Arewa maso Gabas da aka gudanar a Gombe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga, ya fitar, an jaddada aniyar kwamitin wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a jam’iyyar.
Taron ya nuna cewa Tinubu ne kaɗai dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a 2027.
Kungiyar ta jaddada cewa zaɓen mataimakin shugaban ƙasa yana da nasaba da tsarin shugaba ne kai tsaye, yana mai cewa wannan babbar dabara ce da za a yi la’akari da ita don nasarar jam’iyyar.
Ta ce:
"Haƙƙin Shugaban Ƙasa ne kaɗai zaɓar mataimakinsa. Ba wanda zai tilasta masa zaɓar wani mutum; Dole ne ya zaɓi wanda zai iya aiki da shi."
Kwamitin APC ya damu kan rigimar jam'iyya
Da yake bayani kan abin da ya faru, kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai kira da a kwantar da hankali a tsakanin mambobin jam’iyya.
Kungiyar ta ƙara da cewa irin waɗannan abubuwan ba su kamata su hana cigaban da APC ke samu a ƙarƙashin jagoranci na yanzu ba.
"Abin da ya faru a Gombe ba al’adarmu ba ne, kuma ba zai canza tafiyar jam’iyyarmu ba. APC jam’iyya ce mai ƙarfi da haɗin kai a ƙarƙashin Tinubu da Ganduje.
- Cewar kungiyar

Asali: Twitter
Rawar APC a Arewa kan nasarar Tinubu
Kungiyar ta jaddada muhimmancin rawar da shugaban jam’iyya na ƙasa ke takawa wajen tabbatar da adalci da bin kundin tsarin mulki, cewar The Guardian.
Yayin da suka tabo sakamakon zaɓen 2023, kwamitin ya bayyana irin gudummawar da Arewacin Tsakiya ta bayar wajen nasarar APC da Tinubu.
Sun bayyana cewa yankin Kudu maso Yamma da Arewa maso Yamma su ne suka fi ƙoƙari, yayin da Tsakiyar Arewa ta kawo ƙuri’u sama da miliyan 1.7.
"Tare da shugabancin Tinubu da Alhaji Ganduje, APC na hannun ƙwararru. Muna roƙon mambobi da su guji duk wani abu da zai kawo rudani ko katsewar aiki."
- Cewar sanarwar
'Yan jam'iyyar APC sun yi wa Ganduje ihu
Kun ji cewa an gudanar da taron masu ruwa da tsaki na APC a Gombe inda aka samu hatsaniya sakamakon rashin jituwa tsakanin jiga-jigan jam’iyyar.
An gano faifan bidiyo da ya nuna yadda aka yi wa Abdullahi Ganduje ihu da 'ba ma yi' yayin da ya bayyana goyon baya ga Bola Tinubu.
Wasu wakilai sun fusata da yadda aka yi watsi da Kashim Shettima, sun yi zage-zage da tayar da hankali, alamar rikici na shirin barkewa a jam'iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng