Jerin Gwamnoni 8 da Suka Sauya Sheka daga PDP zuwa APC Suna kan Mulki

Jerin Gwamnoni 8 da Suka Sauya Sheka daga PDP zuwa APC Suna kan Mulki

A ranar Juma’a, 6 ga Yuni, Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya sanar da sauya sheƙarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gwamna Eno ya bayyana hakan ne a wani taro na musamman da aka shirya a gidan gwamnati da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Tambuwal, Sheriff da Gwamna Eno.
Gwamnonin da suka koma APC lokacin suna kan mulki Hoto: Sheriff Oborevwori, Aminu Tambuwal, Pastor Umo Eno
Asali: Facebook

Taron ya samu halartar fitattun ‘yan jam’iyyar APC daga sassa daban-daban na ƙasar nan ciki har da gwamnoni, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Jerin gwamnonin da suka koma APC a kan mulki

Wannan ba shi ne karo na farko da gwamna mai ci ya sauya jam'iyyar siyasa ba musamman daga PDP zuwa APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro maku jerin gwamnoni takwas da suka bar PDP zuwa APC a lokacin suna kan madafun iko. Ga su kamar haka:

1. Fasto Umo Eno (jihar Akwa Ibom)

Sauya sheƙar Gwamna Umo Eno zai kawo gagarumin sauyi a siyasar Akwa Ibom, wanda zai iya tasiri sosai a zabukan gaba.

A tarihin siyasar Najeriya, tun da aka dawo mulkin dimokuraɗiyya a 1999, PDP ce kaɗai ke mulki a jihar kafin yanzu da APC ta karɓa.

Gwamna Eno ya koma APC.
Gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a ranar Babbar Sallah Hoto: Pastor Umo Eno
Asali: Facebook

Gwamna Eno ya ce salon mulkin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa ya koma APC, amma ba don wsta gazawa ba.

2. Sheriff Oborevwori (jihar Delta)

A ranar Laraba 23 ga watan Afrilu, 2025, Gwamna Sheriff Oborevwori ya bar PDP zuwa jam'iyyar APC tare da tsohon abokin takarar Atiku, Ifeanyi Okowa.

Wannan sauya sheka ta bai wa mutane da dama mamaki, duba da cewa Delta na daga cikin jihohin da PDP ke rike da su tun 1999.

3. Dave Umahi (Jihar Ebonyi)

A watan Nuwamba 2020, Umahi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a wa’adin mulkinsa na biyu, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Umahi ya bayyana cewa PDP na nuna wariya ga yankin Kudu maso Gabas, sannan ya yabawa APC kan ayyukan gine-ginen more rayuwar da ta yi a yankin a karkashin Buhari.

4. Ben Ayade (Jihar Kuros Riba)

A watan Mayu 2021, Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Ribas ya fice daga jam'iyyar PDP, sannan ya shiga APC.

Gwamnan Ayade, wanda ya sauka daga mulki a 2023, ya ce ya koma APC ne domin daidaita jihar Kuros Riba da gwamnatin tarayya.

5. Bello Matawalle (Jihar Zamfara)

Bello Matawalle ya sauya sheƙa zuwa APC a watan Yuni 2021 bayan rikice-rikicen siyasa da suka addabi Zamfara a lokacin mulkinsa.

Ana ganin dai wannan matakin ya taimaka wajen dawo da daidaito a siyasar jihar Zamfara duk da Matawalle bai samu nasarar tazarce ba a zaɓen 2023.

Gwamna Bello Matawalle.
Bello Matawalle na cikin waɗanda suka koma APC a kan mulki Hoto: Bello Matawalle
Asali: Facebook

6. Aminu Tambuwal (Jihar Sakkwato)

Aminu Waziri Tambuwal na ɗaya daga cikin gwamnonin PDP da suka taɓa sauya sheka zuwa APC lokacin yana kan madafun iko.

Tambuwal ya koma APC kafin babban zaɓen 2015, lokacin da jam'iyyar ta samu nasarar karɓe mulkin Najeriya da jihohi da dama musamman a Arewa.

Sai dai Aminu Tambuwal ya koma PDP a 2018, kuma daga bisani aka danganta shi da yunkurin komawa APC yayin da yake kan mulki.

7. Aliyu Wamakko (Jihar Sakkwato)

Aliyu Wamakko ya shiga APC a shekarar 2014, lokacin da yake kan kujerar gwamnan jihar Sakkwato.

Wamakko na daya daga cikin manyan ƙusoshi na sahun farko da suka bar PDP, wanda hakan ya taka rawar gani wajen nasarar APC a zaben 2015.

8. Abdulfatah Ahmed (Jihar Kwara)

Abdulfatah Ahmed ya sauya sheƙa zuwa APC a shekarar 2014, tare da Bukola Saraki, a lokacin da “guguwar maja," ta sauya siyasar jihar Kwara.

Duk da daga baya ya koma PDP, amma sauya sheƙar da Abdulfatah Ahmed ya yi kafin zaɓen 2015 ta taimaka wajen nasarar ƴan adawa a zaɓen shugaban kasa.

Gwamna Eno ya rasa kwamishina da ya shiga APC

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Umo Eno ya fara rasa kwamishinoninsa ƙasa da awa ɗaya bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Kwamishinan ayyuka na musamman da tashar jiragen ruwa ta Ibom, Mista Ini Ememobong, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Ememobong ya ce ya yi murabus ne saboda bin umarnin gwamnan cewa duk wanda ba zai bi shi zuwa APC ba ya ajiye aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262